GMD ya yi zazzaga a NNPC, an canza wa wasu manyan ma’aikata wuraren aiki, an tsige wani

GMD ya yi zazzaga a NNPC, an canza wa wasu manyan ma’aikata wuraren aiki, an tsige wani

  • Mele Kolo Kyari ya fara kawo wasu tsare-tsare kafin PIB ta kai ga soma aiki
  • Billy Okoye da Aisha Ahmadu-Katagum sun zama manyan Darektoci a NNPC
  • Garba-Deen Muhammad zai maye gurbin Dr. Kennie Obateru a kamfanin man

Abuja - A ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, 2021, kamfanin mai na kasa, ya bada sanarwar kara wa wasu ma’aikata matsayi domin cike guraben da aka bari.

Kamfanin NNPC ya bada sanarwar cewa an kuma canza wa wasu wurin aiki, sannan an sallami wani.

Jaridar Punch ta ce babban jami’in hulda da jama’a na NNPC, Dr. Kennie Obateru, ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar jiya a babban birnin tarayya Abuja.

GMD ya nada sababbin darektoci - Kennie Obateru

Sanarwar ta ce Billy Okoye ya zama sabon darekta na bangaren kasuwanci. Haka zalika ita ma Aisha Ahmadu-Katagum, an kara mata matsayi zuwa Darekta.

Dr. Kennie Obateru ya ce kafin yanzu Mista Billy Okoye da kuma Misis Aisha Ahmadu-Katagum suna rike ne da mukaman Manajoji a kamfanin man na kasa.

Kara karanta wannan

An saki 'dan Yar'adua da ya hallaka mutum hudu da mota a Yola

Har ila yau, sauye-sauyen da aka yi ya shafi Adeyemi Adetunji, wanda a da shi ne babban jami’in gudanar da kasuwanci, yanzu ya dare kujerar babban Darekta.

GMD na NNPC
NNPC GMD Mele Kolo Kyari Hoto: www.tvcnews.tv
Asali: UGC

Mohammed Ahmed wanda shi ma babban jami’in gudanar wa ne, ya zama Darekta a fannin gas.

PIB ta sa an soke mukaman COO, an kawo ED

Sanarwar da ta fito daga bakin Okoye ta ce daga yanzu babu kujerun babban jami’an gudanar wa a NNPC, an maye mukaman ne da kujerun manyan darektoci.

Kamar yadda The Nation ta kawo rahoto, wannan sauyi da aka samu a kamfanin na NNPC, ya na cikin shirye-shiryen da ake yi domin a dabbaka dokar PIB.

A sakamakon wannan garambawul da aka yi, NNPC ta ce an kori Yusuf Usman, wanda a baya yake rike da kujerar babban jami’in gudanar wa a harkar gas.

Bayan haka, Garba-Deen Muhammad zai canji Obateru a kujerar babban jami’in hulda da jama’a. Muhammad ya taba rike kujerar kakakin kamfanin a baya.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan Hausa, Diamond Zahra

Gwamnatin tarayya ta na biyan tallafin man fetur

Kwanaki shugaban kamfanin mai na kasa, Malam Mele Kolo Kyari, ya ce gwamnatin tarayya ta na kashe makudan kudi saboda a rike farashin man fetur.

NNPC ya ce ainihin kudin da ya kamata a rika saida litar man fetur a halin yanzu shi ne N256. Amma gwamnati ta ke kokarin ganin lita bai haura N165 ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel