Wadanda suka sace Kwamishina a Neja sun bukaci 'yanunuwa su hada masu Naira Miliyan 500
- ‘Yan bindiga sun tuntubi ‘yanuwan Kwamishinan yada labarai na jihar Neja
- An yi garkuwa da Alhaji Sani Mohammed Idris daga gidansa cikin tsakar dare
- Ana neman ‘yanuwan Sani Mohammed Idris su biya fansar Naira miliyan 500
Niger - Miyagun da suka tsare kwamishinan harkokin yada labarai na jihar Neja, sun tuntubi ‘yanuwansa, sun bukaci a biya kudin fansa.
Jaridar The Nation ta ce ‘yan bindigan da su ka yi garkuwa da Malam Sani Mohammed Idris, sun fada wa iyalinsa su kawo Naira miliyan 500.
Rahoton da aka fitar a ranar Litinin 9 ga watan Agusta, 2021, ya ce miyagun ‘yan bindigan sun ce sai an biya kudin sannan kwamishinan zai fito.
An yi garkuwa da Sani Mohammed Idris a yau
Kamar yadda ku ka samu labari dazu da safe, an dauke mai girma Kwamishinan ne a kauyensa cikin dare a karamar hukumar Tafa, a jihar Neja.
‘Yan bindigan sun yi awon-gaba da Sani Mohammed Idris a gidansa da ke garin Baban Tunga.
Kwamishinan yada labaran ya na yawan kai ziyara zuwa gida domin duba ganin aikin da ake yi a gonakinsa, sannan kuma ya gana da ‘yanuwansa.
Dauke kwamishinan ya sa mataimakin gwamna, Ahmed Muhammad Ketso ya jagoranci taron harkar tsaro na musamman da aka shirya a dazu.
Bisa dukkan alamu, gwamna ba ya jihar, don haka mataimakin gwamnan jihar Neja, Alhaji Ahmed Muhammad Ketso ya kira zaman gaggawa.
Har zuwa yanzu babu labari daga jami’an tsaro da hukumomi cewa an ceto wannan Bawan Allah, kuma ‘yanuwansa ba su bayyana halin da ake ciki ba.
An yi gaba da Kwamishinan labarai - SSG
Bayan abin ya faru, an ji Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana cewa jami’an tsaro su na kokarin ceto kwamishinan.
Manema labarai sun nemi jin ta bakin kakakin ‘yan sanda na Neja, SP Wasiu Abiodun, amma ba a dace ba.
Asali: Legit.ng