Hukumar Kwastam ta damke buhuhunan Shinkafa 314, buhuhunan dabino da Masara, a jihar Katsina

Hukumar Kwastam ta damke buhuhunan Shinkafa 314, buhuhunan dabino da Masara, a jihar Katsina

  1. Hukumar Kwastam tayi babban kamu a jihar Kastina
  • Har yanzu gwamnatin Buhari ta haramta shigo da shinkafa yar waje
  • Hukumar ta ce ta gano wasu dabarun da masu fasa kwabri keyi wajen shigo da kaya

Hukumar Kwatsam ta sanar da cewa ta damke motoci 13, buhuhunan Shinkafa 314 da wasu kayayyaki da kudin dutinsu ya kai milyan 60 a jihar Katsina.

Hukumar ta yi wannan kamu ne cikin wata guda tsakanin ranar 8 Yuli da 3 ga Agusta.

Mukaddashin Kontrolan Kwastam na jihar Katsina, Dalha Wada, ya bayyana hakan ranar Talata a Kaduna yayin hira da manema labarai kan nasarorin da yankinsa ta samu, Punch ta ruwaito.

A cewar Wada, a cikin wata guda, hukumar ta kama motar kirar Lexus 2011, da Toyota Corolla 2015.

Wada yace:

"Hukumar ta damke manyan buhuhunan Shinkafa 314 mai kimanin kudi N7.5m, galolin man gyada 25ltr guda 227 mai kimanin kudin N715,000 da katon na taliyar waje 178 mai kimanin kudi N961,000."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

Wada ya kara da cewa sun damke Dabino mai kumanin kudi N2.2m, da waken Soya na kimanin kudi N262,000.

A cewarsa, hukumar na iyakan kokarinta wajen hana masu fasa kwabri shigowa Najeriya.

Hukumar Kwastam
Hukumar Kwastam ta damke buhuhunan Shinkafa 314, buhuhunan dabino da Masara, a jihar Katsina Hoto: NCS
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng