NNPC ta ce za a koma shan man fetur a kan sama da N250 da zarar an janye tallafin mai

NNPC ta ce za a koma shan man fetur a kan sama da N250 da zarar an janye tallafin mai

  • Sai da ta kai NNPC ta na samun gibin N150bn wajen biyan tallafin man fetur
  • Mele Kolo Kyari yace an kawo dabarar da ta sa aka rage man da ake sha a rana
  • Akwai ranar da aka sha lita miliyan 103 saboda fita da fetur zuwa makwabta

Shugaban kamfanin mai a kasa watau NNPC, Malam Mele Kolo Kyari, ya ce gwamnatin tarayya ta na kashe makudan kudi saboda a rike farashin litar fetur.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Mele Kolo Kyari ya na cewa duk wata sai gwamnatin Najeriya ta batar da Naira biliyan 140 zuwa biliyan 150 a kan tallafin mai.

NNPC ya ce ainihin kudin da ya kamata a rika saida litar man fetur a halin yanzu shi ne N256. Amma gwamnati ta ke kokarin ganin an cigaba da saye a N162.

KU KARANTA: Karin kudin litar man fetur ya riga ya zama dole - MAN

N150bn ya na tafiya wajen tallafin man fetur

Mele Kyari ya ce:

“Idan za mu saida fetur a kan kudin da yake yau a kasuwa, za mu rika saida lita ne a kan kusan N256. Abin da mu ke saida wa shi ne N162.”

Shugaban na NNPC ya tabbatar da cewa gwamnatin kasa ta ke cika gibin da aka samu tsakanin asalin farashin fetur a kasuwa da kuma abin da al’umma ke saye.

“Bambancin kudin da ake samu ya na kai N140bn zuwa N150bn a kowane wata.” Inji GMD na kamfanin.

Kyari ya ce a yanayin man da ake sha a yau, gwamnati ba ta da kudin da za ta cigaba da biyan biliyoyi a matsayin tallafi, hakan ya sa aka rage fasa-kauri.

GMD NNPC
GMD NNPC, Mele K. Kyari Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Shaukin Muhammadu Buhari ya sa Marubuci ya rubuta littafi a kansa

Ana fasa-kaurin fetur zuwa kasashen makwabta

Kamar yadda Vanguard ta fitar da rahoto a ranar 23 ga watan Yuni, 2021, ana zargin cewa ana fita da fetur daga Najeriya zuwa wasu kasashen makwabta a Afrika.

Hakan ya sa adadin litocin man da ake sha a duk rana ya iya kai lita miliyan 103 a watan Mayu.

A cewar Kyari, tsarin Operation White da aka shigo da shi, da hada-kai da hukumar EFCC ya taimaka wajen rage adadin man da ake sha zuwa lita miliyan 60.

A yau kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta na kokarin sauko da farashin shinkafa ya yi kasa, amma lamarin ya ci tura, inda 'yan kasuwa su kace kaya sun tashi.

Kungiyar RIPAN ta bada uzuri kan abin da ya sa buhun shinkafa ya kai N23, 000, ta ce an daina samun bashi daga CBN, kuma Dala ta tashi, sannan mai ya kara kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng