Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Talata a matsayin 1 ga watan Muharram

Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Talata a matsayin 1 ga watan Muharram

  • Sarkin Musulmi ya ayyana Talata, 10 ga Agusta, a matsayin ranar farko na Muharram 1443AH
  • Don haka, ranar Talatar ta zama sabuwar shekarar Musulunci ta 1443AH
  • Mai alfarma Sarkin Musulmi ya taya Musulman Najeriya murnar sabuwar shekara tare da yi musu fatan samun jagoranci da albarkan Allah

An aika sako zuwa ga Musulman Najeriya. Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ne ya aika da sakon.

A cikin sakon, basaraken kuma jagoran musulmi ya ayyana ranar 10 ga watan Agusta, a matsayin ranar farko ta Muharram 1443AH.

Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Talata a matsayin 1 ga watan Muharram
Ranar Talata, 10 ga watan Agusta ne 1 ga watan Muharram Hoto: @sultanatecouncill
Asali: Facebook

Sanarwar ta zama Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1443AH, za ta fara a ranar Talata, VON ta ruwaito.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa Abubakar III ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Farfesa Sambo Junaidu ya fitar ranar Lahadi.

Bangare na sanarwar ta ce:

"Sarkin Musulmi ya karbi rahoton kuma a bisa haka ya ayyana Talata, 10 ga Agusta, a matsayin ranar farko ta Muharram, 1443 AH."

Kara karanta wannan

Jerin jihohin da suka bada hutu don murnar sabuwar shekarar Musulunci 1443

Da yake ci gaba, sarkin ya taya Musulmin Najeriya murna tare da yi musu fatan Allah ya yi musu jagora da albarka.

Hukumomin Saudi Arabia sun sanar da bude wa Musulman Duniya kofar yin aikin Umrah

A wani labarin, Hukumar dillacin labarai na kasar Saudi Arabia ta ce za ta bada dama ga sauran musulmai daga kasashen waje su cigaba da ibadar Umrah.

An dawo Umrah a ranar 1 ga watan Muharram, 1443 A ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, 2021, hukumar SPA ta kasar Saudi Arabia ta rahoto cewa za a cigaba da yin Umrah a yau, ranar 9 ga watan Agusta, 2021.

Hukumomin Saudiyya za su bude kofa ga maniyyatan da aka yi wa allurar rigakafin cutar COVID-19. Reuters ta fitar da wannan rahoto a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel