Jerin jihohin da suka bada hutu don murnar sabuwar shekarar Musulunci 1443

Jerin jihohin da suka bada hutu don murnar sabuwar shekarar Musulunci 1443

Ranar farkon sabuwar shekarar Hijra zai kama ranar Litinin ko Talata dangane da ranar da aka ga wata.

Don murnar wannan shekara ta 1443 bayan Hijra, wasu jihohin Najeriya sun bada hutu ga al'ummarsu.

Legit ta hararo muku jihohi biyar da za'a yi hutu don murnar ranar:

1. Jihar Osun

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya sanar da ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci - Hijrah 1443 AH.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Kwamishanan harkokin cikin gidan jihar, Tajudeen Lawal, ranar Juma'a a Osogbo, rahoton NAN.

2. Jihar Oyo

Gwamnatun jihar Oyo, ta sanar da ranar Talata, 10 ga watan Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci - Hijrah 1443 AH.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Sakataren gwamnatin jihar, Mrs Olubamiwo Adeosun, ta saki ranar Juma'a a Ibadan, babbar birnin jihar, rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Wanda ya kashe mutum hudu a hadarin mota ba 'dan Umaru Yar'adua bane, dan Shehu Yar'adua ne

Gwamnan ya yi kira ga Musulmai da masu bin sauran addinai suyi amfani da hutun domin addu'a ga cigaban jihar da Najeriya gaba daya.

Jerin jihohin da suka bada hutu don murnar sabuwar shekarar Musulunci 1443
Jerin jihohin da suka bada hutu don murnar sabuwar shekarar Musulunci 1443

3. Jihar Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya alanta ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci - Hijrah 1443.

Wannan na kunshe cikin jawabin da kwamishanan labaran, Muhammad Garba, ya saki ranar Juma'a

4. Jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da ranar Litinin, 9 ga Agusta, a matsayin ranar hutu don murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci.

Ya yi kira da mutan jihar suyi amfani da wannan dama wajen yiwa jihar addu'a kan halin rashin tsaron ake ciki.

5. Jihar Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu ya bi sahun takwararorin na bada hutun sabuwar shekarar Musulunci.

Wannan na kunshe cikin jawabin da aka saki a birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Kashe-kashen dake faruwa a Plateau ya saba dokokin Allah, Malaman addinai sun yi tsokaci

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng