Hukumomin Saudi Arabia sun sanar da bude wa Musulman Duniya kofar yin aikin Umrah

Hukumomin Saudi Arabia sun sanar da bude wa Musulman Duniya kofar yin aikin Umrah

  • Hukumomin kasar Saudi Arabia sun bada dama a cigaba da zuwa aikin Umrah
  • Daga yau duk wanda ya yi rigakafin COVID-19 zai iya ibada a kasa mai tsarkin
  • An dauki tsawon lokaci mutanen kasar waje ba su yi Umrah a Saudi Arabia ba

Saudi Arabia - Hukumar dillacin labarai na kasar Saudi Arabia ta ce za ta bada dama ga sauran musulmai daga kasashen waje su cigaba da ibadar Umrah.

An dawo Umrah a ranar 1 ga watan Muharram, 1443

A ranar Lahadi, 8 ga watan Agusta, 2021, hukumar SPA ta kasar Saudi Arabia ta rahoto cewa za a cigaba da yin Umrah a yau, ranar 9 ga watan Agusta, 2021.

Hukumomin Saudiyya za su bude kofa ga maniyyatan da aka yi wa allurar rigakafin cutar COVID-19. Reuters ta fitar da wannan rahoto a ranar Lahadi.

Daga adadin maniyyata 60, 000 da su ka yi aikin hajjin shekarar bana, za a samu mutane kimanin miliyan biyu da za su rika yin Umrah a duk wata a Saudiyya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 20 da na sani game da Limamin Masallacin Quba Sheikh Zarban, Dr Ibrahim Disina

Za a cigaba da bin dokokin yaki da COVID-19

Rahoton ya tabbatar da cewa masu ibadar za su rika bin matakan yaki da Coronavirus a masallatai da sauran wuraren ziyara domin guje wa cutar.

Masu Umrah daga gida da sauran kasashen waje za su gabatar da takardar da ke nuna an yi masu rigakafin cutar COVID-19, da takardar neman iznin yin ibada.

Saudi Arabia
Masu sauke farali a Saudi Hoto: www.reuters.com
Asali: UGC

Jami’an ma’aikatar Hajj da Umrah na kasar Saudi sun ce akwai jerin wasu kasashe da ba za a bar mutanensu su shigo kai tsaye, ba tare da an killace su ba tukuna.

A watan Oktoban shekarar da ta wuce ne aka fara kyale mutanen Saudi Arabia su yi aikin Umrah bayan an dakatar da ibadar saboda yaduwar ciwon Coronavirus.

Shekara biyu kenan ana takaita adadin wadanda suke zuwa kasa mai tsarkin da nufin sauke farali. A watan Yulin da ya wuce, ba a bar ‘yan waje sun yi Hajji ba.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

Dauke wannan takunkumi ya zo ne a lokacin da aka shiga sabuwar shekarar musulunci na 1443.

Idan har za ku tuna, hukumomin kasar Saudiyya sun sa doka cewa mazauna cikin kasar ne kadai za a bari su iya gudanar da aikin Hajji na shekarar da ta gabata.

Ko a mazaunan, sai wanda ya yi rigakafin COVID-19 akalla sau daya, kuma ya yi kwana 14 da karbar allurar ko wanda ya warke daga cutar aka ba wannan dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel