Gwamnatin Buhari ta fusata, ta ce duk likitan da ya shiga yajin aiki ba shi ba albashi

Gwamnatin Buhari ta fusata, ta ce duk likitan da ya shiga yajin aiki ba shi ba albashi

  • Wani sabon rikici tsakanin gwamnati da likitocin Najeriya ya kara bayyana a makon nan
  • Gwamnati ta ce ba za ta sake biyan duk wani likitan da ya shiga yajin aikin kungiyarsu ba
  • Kungiyar likitoci kuwa ta ce ba za ta razana ba, don haka ta kara kalubalantar gwamnati

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta umarci manyan lokictoci a asibitocin koyarwa da su bude kundin rajista da zai ke ba da bayanai kan likitoci da ke yajin aiki a wani mataki na daina biyan su albashi, BBC Hausa ta ruwaito.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce daga gobe Talata dokar 'ba-aiki ba-albashi' za ta fara aiki kan duk wani likitan da ya amsa kiran kungiyar likitoci na shiga yajin aiki.

Wannan rikici tsakanin gwamnati da likitoci na haifar da barazana ga marasa lafiya da dama a asibitoci inda tun a makon da ya gabata mutane ke ta kwashe 'yan uwansu da ke jinya daga asibitoci saboda rashin samun kulawar kwararru.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin NARD: Kungiyar Likitoci Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Sallami Wasu Ministocinsa

Gwamnatin Buhari ta fusata, ta ce duk likitan da ya shiga yajin aiki ba shi ba albashi
Likitocin Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Meye ya jawo haka?

A ranar Litinin din makon da ya gabata likitocin suka koma yajin aiki da suka dakatar a ranar 10 ga watan Afrilu bayan alkawarin da gwamnati tayi musu na biya musu bukatunsu, ciki harda biyansu wasu kudade da alawus-alawus dinsu ya ci tura.

Sai dai a cewar likitocin bayan cika kwanaki 100 da wadannan alkawurra gwamnati ta gaggara biya musu bukatunsu, dalilan da suka tunzurasu sake komawa yajin aikin kenan.

Shugaban kungiyar likitocin ta NARD, Dr Uyilawa Okhuaihesuyi ya ce ba su razana da barazanar gwamnati ba domin babu yadda za a yi gwamnati ta iya maye gurbin likitoci 16,000 da sabbi.

Yajin Aikin NARD: Kungiyar Likitoci Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Sallami Wasu Ministocinsa

Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD), Uyilawa Okhuaihesuyi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sallami duk wanda ke da hannun a yajin aikin da likitoci ke yi a kasar nan.

Kara karanta wannan

Ngige: Na ja kunnen 'ya'yana likitoci da kada su shiga yajin aikin nan na rashin hankali

Okhuaihesuyi yace ya kamata a sallami ministan kwadugo, Chris Ngige, ministan lafiya, Osagie Ehanire, da kuma shugaban MDCN, Tajuddeen Sanusi, matukar ba zasu iya sauke nauyin dake kansu ba.

The Cable ta ruwaito cewa a ranar 2 ga watan Agusta, likitocin suka tsunduma yajin aiki bisa rashin biyansu albashi, da wasu alawus da dai sauransu.

A yanzu kam manufar mu ita ce sama wa 'yan Najeriya aiki, in ji Gwamnatin Buhari

A wani labarin daban, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin jam'iyyar APC karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fifita samar da ayyukan yi a kasar cikin shekara guda.

Osinbajo, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Laolu Akande, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da yada labarai, ya aikewa Legit.ng.

Ya ce gwamnatin tarayya ta fifita bukatar samar da ayyukan yi a dukkan manyan manufofinta, ayyukanta da shirye-shiryenta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel