Shugabannin masu hada bama-bamai na Boko Haram, Mala Musa da Abu Darda sun tuba

Shugabannin masu hada bama-bamai na Boko Haram, Mala Musa da Abu Darda sun tuba

  • Hatsabibin shugaban masu hada bama-bamai na Boko Haram, Mala Musa Abuja tare da mataimakinsa Abu Darda sun tuba
  • Tsoffin 'yan Boko Haram din sun mika kansu tare da makamansu da kuma iyalansu ga sojojin Najeriya dake Bama
  • Tsabar ragargazar da sojoji ke musu har maboyarsu da sansanoninsu ne ya hana su sakat inda kwanciyar hankali tayi musu kaura

Bama, Borno - Sakamakon yadda ake tsanantawa 'yan ta'adda da dakarun rundunar operation HADIN KAI ke yi ga 'yan ta'adda, hakan yasa miyagun 'yan Boko Haram dake arewa maso gabas suke cigaba da mika wuya tare da tuba.

Gagarumin dan ta'addan da ya kware a hada bama-bamai, Musa Adamu wanda aka fi sani da Mala Musa Abuja da mataimakinsa Usman Adamu wanda aka fi sani da Abu Darda tare da iyalansu da mabiyansu duk sun tuba inda suka mika makamansu ga sojoji a Bama dake jihar Borno, prnigeria ta ruwaito.

Shugaban mai hada bama-bamai na Boko Haram ya tuba tare da yaransa, ya mika wuya ga sojoji
Shugaban mai hada bama-bamai na Boko Haram ya tuba tare da yaransa, ya mika wuya ga sojoji. Hoto daga prnigeria.com
Asali: UGC

An karba tubabbun tare da GOC

Mukaddashin babban kwamnadan Div 7 da kwamandan OPHK Brigadier General Abdulwahab Adelokun Eyitayo yana hedkwatar birged dake Bama a ranar Asabar, 7 ga watan Augusta yayin da aka karba tubabbun 'yan Boko Haram din da iyalansu, prnigeria ta wallafa.

A yayin ziyarar, GOC yace hukuncin yadda makaman tare da fitowarsu abun jinjinawa ne inda ya kara da cewa su yi wa 'yan uwansu magana dake daji da su zo tare da rungumar sabuwar rayuwar kwanciyar hankali.

Janar Eyitayo da yayi magana da yawun wani tafinta inda ya ce gwamnati zata karba tubabbun a gyara su kafin a barsu su koma cikin jama'a su cigaba da rayuwa.

Yayin rarraba musu sabbin kaya da kayan abinci, an gano cewa tsananta samamen da dakarun sojin ke yi ta hanyar kai musu farmaki ta tabbatar da samuwar yunwa, rashin kwanciyar hankali, tashin hankalin cikin gida, cutuka tare da matsi ga 'yan ta'addan.

'Yan sanda sun samo N3m da mota daga wacce ake zargi da sheke wani matashi

Hukumar ‘yan sandan jihar Akwai Ibom sun ce sun samu kusan naira miliyan 3 da wata mota kirar 4matic Mercedes Benz daga hannun wata Loretta Anoh, wacce ake zargin ta kashe wani Chikoka Henry mai shekaru 36 a cikin gidansa.

An tsinci gawar Henry a cikin jini wanda ake zargin ya zuba ne sakamakon yankar da aka yi masa, yayin da aka nemi motarsa kirar 4matic Mercedes Benz mai lamba EKY 694 GP aka rasa.

Kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar an ga gawarsa ne bayan dan uwansa, Collins Okpara ya kai kara akan ganin gawar dan uwansa a gidansa dake Uyo bayan ya neme shi bai same shi ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel