'Yan sanda sun samo N3m da mota daga wacce ake zargi da sheke wani matashi

'Yan sanda sun samo N3m da mota daga wacce ake zargi da sheke wani matashi

  • Hukumar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta samu akalla naira miliyan 3 da wata mota kirar marsandi daga hannun wata Loretta Anoh
  • Ana zargin Loretta da kisan wani Chikoka Henry mai shekaru 36 har cikin gidansa bayan an gan shi kwance cikin jini
  • Saidai bayan ya kan da aka yi masa ba a ga motarsa ba sai kawai aka ganta a hannun Loretta bayan dan uwansa ya kai kara

Uyo, Akwa Ibom - Hukumar ‘yan sandan jihar Akwai Ibom sun ce sun samu kusan naira miliyan 3 da wata mota kirar 4matic Mercedes Benz daga hannun wata Loretta Anoh, wacce ake zargin ta kashe wani Chikoka Henry mai shekaru 36 a cikin gidansa.

An tsinci gawar Henry a cikin jini wanda ake zargin ya zuba ne sakamakon yankar da aka yi masa, yayin da aka nemi motarsa kirar 4matic Mercedes Benz mai lamba EKY 694 GP aka rasa.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun gurfanar da wani Matashi da ake zargi ya saci N10.7bn a hannun mutane 170

'Yan sanda sun samo N3m da mota daga wacce ake zargi da sheke wani matashi
'Yan sanda sun samo N3m da mota daga wacce ake zargi da sheke wani matashi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Dan uwan mamacin ne ya kaiwa 'yan sanda rahoto

Kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar an ga gawarsa ne bayan dan uwansa, Collins Okpara ya kai kara akan ganin gawar dan uwansa a gidansa dake Uyo bayan ya neme shi bai same shi ba.

Bisa binciken ‘yan sanda an gane cewa wacce ake zargin, Loretta Anoh ce mutum ta karshe da ta kai masa ziyara a ranar 3 ga watan Augustan 2021, Daily Trust ta ruwaito.

An kama wacce ake zargi da kudaden da mota

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’ar ‘yan sandan, SP Odiko Macdon, ya sanya hannu a ranar Juma’a, bincike ya nuna cewa an samu N2,943,250 daga hannun wacce ake zargin kuma ta furta da kanta cewa ta saci kudin a hannun mamacin.

Macdon ya ce wacce ake zargin tana tsaka da mayar da 4matic Mercedes Benz din da ta sata tata kafin a kamata.

Kara karanta wannan

Karantsaye ga tsaro a gidan gwamnatin Borno: Shugaban wata NGO ya shiga hannun hukuma

A ranar 4 ga watan Augustan 2021 da misalin karfe 9:10am bayan wani Collins Okpara na layin Afaha a Uyo ya nemi dan uwansa Chikoka Emeka Henry mai shekaru 36 ta waya amma bai same shi ba sai ya yanke shawarar kai masa ziyara a gidan Chikoka dake No. 2 Osongama Estate dake Uyo.
Bayan isarsa ne ya ga gawarsa kwance lame-lame cikin jini. Kuma ya sanar da ‘yan sanda cewa ya nemi motarsa kirar 4matic Mercedes Benz mai lamba EKY 694 GP amma bai ganta ba a inda ake ajiyewa.

Daily Trust ta wallafa cewa, bayan haka ne ‘yan sanda suka zurfafa bincike kafin suka gano ta saci N2,943,250 kuma da bakinta ta fura hakan.

Mutum 1 ya sheka lahira yayin da 'yan fashi suka kai farmaki bankuna 2

Wani rahoto da ya fito daga jaridar The Nation ya bayyana yadda wasu miyagun 'yan fashi da makami a ranar Alhamis, 5 ga Augusta suka kai farmaki wasu bankuna biyu dake Iree, karamar hukumar Boripe ta jihar Osun.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

Jaridar ta kara da cewa an sheke mutum daya yayin da 'yan fashin suka kutsa yankin wurin karfe 3 da minti hamsin na rana kuma suka dinga harbe-harbe.

Wani mazaunin yankin mai suna Fisayo ya ce 'yan fashin sun dinga harbe-harbe domin tsorata jama'a kafin su shiga bankunan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng