Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Masu Garkuwa, Sun Kame Wasu a Benuwai

Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Masu Garkuwa, Sun Kame Wasu a Benuwai

  • Rundunar yan sanda reshen Benuwai ta sanar da kuɓutar da wani hamshakin ɗan kasuwa da aka sace
  • Rundunar ta kuma bayyana cewa ta samu nasarar hallaka ɗaya daga cikin ɓarayin tare da kame wasu biyu
  • Kakakin yan sandan jihar, Sewuese Anene, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar

Benue:- Rundunar yan sanda ta jihar Benuwai, ta bayyana samun nasarar sheke wani da ake zargin ɗan garkuwa ne tare da kame wasu biyu, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Kakakin yan sandan jihar, DSP, Sewuese Anene, yace ɗan ta'addan ya mutu ne a asibiti bayan samun raunuka yayin artabu da jami'an yan sanda.

Tribune ta ruwaito cewa waɗanda ake zargin sun sace wani ɗan kasuwa, Peter Ogbonna, daga shagonsa dake Ugba, karamar hukumar Logo ranar 29 ga Yuli.

Yan sanda sun kuɓutar da ɗan kasuwa a Benuwai
Gwarazan Yan Sanda Sun Ragargaji Masu Garkuwa, Sun Kame Wasu a Benuwai Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yan sanda sun yi gumurzu da ɓarayin

Jami'an rundunar operation Zenda sun kuɓutar da mutumin bayan fafatawa da masu garkuwan, inda suka kame wasu.

Wani sashin jawabin yace:

"A yau 4 ga watan Agusta mun samu bayanin cewa yan bindigan da suka sace Mr Peter Ogbonna, sun boye a Tse Atoov, Alabaar, karamar hukumar Logo. Nan take jami'ai suka fita zuwa wurin."
"Daga ganin yan sandan sai aka fara musayar wuta amma jami'ai suka ci karfinsu sannan suka kame mutum uku nan take."
"Ɗaya daga cikinsu yaji manyan raunuka inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa a asibiti yayin da sauran mutum biyu Yakyuur Aondona da Teryange Miyina suna cigaba da amsa tambayoyi."

Yan daba sun kashe dalibin kwaleji

A wani labarin kuma Wasu Yan Daba Sun Gutsire Kan Dalibin Kwalejin Fasaha a Kwara

Wasu da ake zargin yan ƙungiyar daba ne sun kashe ɗalibin kwalejin fasaha ta jihar Kwara mai suna, Olawale.

Dailytrust ta ruwaito cewa yan daban, waɗanda suke ƙungiyar adawa, sun farmake shi ne jim kaɗan bayan ya bar gida ranar Talata.

An gano kan ɗalibin a shataletalen Unity a Ilorin bayan mahaifiyarshi ta shafe awanni tana neman ɗan nata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel