Abubuwa 20 da na sani game da Limamin Masallacin Quba Sheikh Zarban, Dr Ibrahim Disina

Abubuwa 20 da na sani game da Limamin Masallacin Quba Sheikh Zarban, Dr Ibrahim Disina

Bauchi - Shugaban gidan Talabijin Sunnah TV, Dr Abu Aisha Ibrahim Disina, ya lissafo wasu abubuwa da ya sani game da marigayi babban Masallacin Quba a Saudiyya wanda ya rasu ranar Juma'a, 8 ga Agusta, 2021.

Na kasance Yaro mai masa Hidima da dawainiya kimanin shekara ashirin da suka gabata tun ina shekarar farko a Jami'a kamar yadda tun shekarar farkon duk yadda yaje a Nigeria ina tare da shi a matsayin dan rakiya mai masa hidima.

(1) Ya san Nigeria da banbance banbancenta kudu da arewa, Hausawa da Yarabawa sama da mafi yawan 'Yan Nigeria.

(2) Shine sanadin yawaitar 'yan arewa a Jami'ar Musulunci ta hanyar fadada guraren Daura (Bita) a garuruwan Sokoto da Maiduguri da Bauchi maimakon Kano da Ilorin kadai a da can!

(3) Yana sane tare da tunawa da yadda akayi ya zabo wassu dalibai zuwa Madina kamar su Sheik Ja'afar da Dr Muhd Sani R/lemo wadanda sukayi fice a fagen Da'awah.

Kara karanta wannan

A karshe IBB ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da ‘mugun gwani’ da Maradona

(4) Ya kyautata alaka tsakanin gwamnatocin Jihohi da Jami'ar Musulunci ta Madina ta hanyar Ziyartarsu gabatar da kyauta ta Musamman, Taryarsu da girmamasu a Madina dss.

(5) Alakarsa da Da'awah a Nigeria ba aikar gwamnatin Saudi ba nee, abu ne da ya sa kansa ya ke kuma fatan samun lada a wajen Allah domin mafi yawa abubuwan da ya gabatar abubuwa ne daga kashin kansa da kansa da abokan taraiyyarsa.

(6) Har a Madina, Ya maida 'yan Nigeria komai nasa domin da yawa cikin hudubobinsa da littafansa 'yan Nigeria ke rubuta masa a keken rubutu kamar su Dr Muhd Sani, Dr Birnin Kudu, Abokina Dr Jamilu Sadisu Zaria.

(7) Yana Mu'amalantar kowa bisa darajarsa, Kullum maganarsa kan Dr Sani wai sun daukoshi daga Nigeria bayan ya zama malami, ko yace da karatunsa muka sameshi, Yana yabo kan kwakwalwar Dr Basheer Aliyu da Nagarta da halin kwarai na Dr Birnin Kudu tare da dattakun Sheikh Abdulwahab Abdallah, amma Ni kuwa da Dr Jamilu Sadisu Zaria duk wani wasan da Kaka ke yiwa jika yana yi da mu.

Kara karanta wannan

Ana batun karbar cin hancin Abba Kyari, magajin shi zai karbi kyautar $10,000

(Ya san bayanan rayuwar dalibansa dalla-dalla, Ya kan ce Mu mutanen Bauchi muna kama Malamai ta hanyar auratayya don duk wadannan Malaman sunyi aure daga Bauchi; Malam Ja'afar, Dr Mansoor sokoto, Dr Muhd Sani Rijiyar Lemo, Dr Abubakar Sani Birnin Kudu da kuma wani da ya kufce bai aura ba, Malam ya san abubuwan da sukafi wadannan nisa kan 'ya'yansa a Nigeria.

(9) Duk cikin Manyan Kasarnan karankaf( Yan siyasa da Attajirai) babu wanda Sheikh ke kauna da Mu'amala ta kud da kud har rasuwarsa kamar Dr Ahmad Adamu Mu'azu( Tshohon Gwamnan Bauchi) saboda halaccin da ya gwadawa Malaman Jami'a da Ziyara da tuntuba da duk abinda aka bukaceshi har zuwa rasuwar Malam, Malam na masa addu'a da masa fatan alkairi ko da yaushe.

(10) Kaunarsa da mutanen Nigeria ta sanyashi har yana kokarin gabatar da jawabai lokacin rufe taron Daura da rubutacciyar Hausa wacce ake rubuta masa da ajamin larabci, kamar yadda kuna haduwa da shi ko kukayi waya da shi Hausa zai fara maka har sai ya tike gabani ya koma larabci.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

Abubuwa 20 da na sani game da Limamin Masallacin Quba Sheikh Zarban, Dr Ibrahim Umar Disina
Abubuwa 20 da na sani game da Limamin Masallacin Quba Sheikh Zarban, Dr Ibrahim Disina Hoto: Ibrahim Disina
Asali: Facebook

(11) Malam ya kyautar da labirarensa(Littattafansa) sama da kwali dari wa al'ummar Nigeria, wadanda a halin yanzu suke karkashin kulawar Dr Abubakar Birnin kudu a birnin Dutse a Jihar Jigawa.

(12) Shedawar kowa ne yadda ya ke bugawa Manyan Almajiransa waya ya gaishesu da mahalarta karatun Tafsirin da suke gabatarwa a Ramalana da Musu Nasiha.

(13) Loakacin rasuwar Malam Ja'afar ya taka rawa wajen kwantar da hankalin malamanmu tare da ba su tabbaci kan cewa zubar jininsa shayarwa ce ga Da'awah.

(14) Sai a wannan Shekarar Sheikh Zarban ya gamsu da jagorancina a Sunna Tv, bayan Sheikh Abdulwahab ya masa dogon bayani kan amfaninta, sakamakon tun bayan kafata bai zo Nigeria ba saboda rashin lafiya, abinda ya ke gudu kar gudanarwa ya hanani karantarwa. Abinda yafi kaunar yaga kanayi karatu da karantarwa kadai.

(15) Dr Basheer Aliyu Alfurqan ya zamo dan cikin gida, don ya kai wassu abubuwa kan 'yayan Sheikh Zarban duk da suna Madina hi kuma yana Nigeria da shi ake gudanarwa.

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna a Kano ya sha alwashin gina 'Film Village' idan ya ci zabe

(16) Sheikh Zarban na matukar kaunar rayuwar kauye da Karkara a Nigeria, wannan ya sa in yana Nigeria mu kan je kasuwannin kauye da shi, yana cinikin dabbobi da fada min yadda ake gane dabbobi masu maiko da wassu abubuwa na da ban.

(17) Karkararsu daya da Sheikh Huzaifi(Limamin masallacin Madina) kuma Malaminsu daya kuma suna auren yayaan Malamin na su kamar yadda karatun kur'aninsu ke kama da juna, Sheikh Zarban ya ce min kwaikwayon muryar malaminsu su ke.

(18) Yana Ziyartar Malaman da ba sa kan hanyar da ya ke kai( Sunnah Salafiyyah) , Yana ziyararsu da gani da Ido kan lamuran akidarsu da kyakykyawar Mua'amala, Misali a Kano ya Ziyarci Sheikh Nasiru Kabara da Sheikh Ishaqa Rabiu dss.

(19) Kullum nasiharsa garemu ku rungumi karantarwa da kyautata Mu'amala da hukumomi tare da gujewa duk wani abindaya ke fito na fito ne da su.

Kara karanta wannan

A yanzu kam manufar mu ita ce sama wa 'yan Najeriya aiki, in ji Gwamnatin Buhari

(20) Sakin fuska da kyauta kuwa ba a magana don ni shaida ne!!!

Ni dai shine ubana na biyu!!

Allah ka yi rahama wa malaminmu malamin malamanmu masoyin al'ummata da ya shuka mata Alkhairai ameen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel