‘Yan Sanda sun gurfanar da wani Matashi da ake zargi ya saci N10.7bn a hannun mutane 170

‘Yan Sanda sun gurfanar da wani Matashi da ake zargi ya saci N10.7bn a hannun mutane 170

  • Jami’an tsaro sun shigar da karar Joshua Kayode kan zargin damfarar N10bn
  • Ana tuhumar wannan matashin mai shekara 22 da laifin cin kudin mutum 170
  • Za a cigaba da tsare Kayode a gidan kurkuku kafin a nemi kotu ta bada belinsa

Legas - Jami’an ‘yan sanda sun gurfanar da wani mutum mai suna, Joshua Kayode a gaban babban kotu da ke Ikoyi, jihar Legas, bisa zargin damfara.

Joshua Kayode ya ci N10.7bn

Kamar yadda Punch ta fitar da rahoto a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta, 2021, ana tuhumar Joshua Kayode da laifin damfarar kudi Naira biliyan 10.7.

Joshua Kayode mai shekara 22 da haihuwa, ya fito da wani tsarin kasuwanci na bogi ne wanda ya yi amfani da shi, ya rika damfarar Bayin Allah har 170.

Rahoton ya ce an gurfanar da Kayode a gaban Alkali mai shari’a, Tijjani Ringim, aka kuma karanto masa laifuffuka 170 da ake zarginsa da aikata wa.

Kara karanta wannan

Da aka je aka dawo, BOT ta ceci Shugaban PDP daga yunkurin tsige shi, a nada rikon kwarya

Zargin da ke kan wuyan matashin su ne karbar kudi ta hanyar yaudara tare da wani kamfaninsa mai suna Quintessential Investment Company Limited.

Lauyan da ya shigar da kara, Williams Tijjani, ya bayyana cewa wannan mutum ya aikata wadannan laifuffuka ne tsakanin Yulin 2020 da Maris 2021.

‘Yan Sanda sun gurfanar da wani Matashi da ake zargi ya saci N10.7bn a hannun mutane 170
Babban kotun Legas da ke Ikoyi Hoto: www.today.ng
Asali: UGC

“Wanda ake tuhuma ya damfari mutane da sunan za su samu riba a wani kasuwanci da za a yi."
"Laiffukan da ya yi sun saba wa sasa na 8 da na 1 na dokokin sata na da makamantan laifuffuka; Advance Fee Fraud and other Fraud Related Offenses Act na shekarar 2006.”

Wanda ake tuhuma zai cigaba da zama a kurkuku

Sai dai Joshua Kayode ya musanya duk wannan zargi da ake yi masa, ya ce bai aikata laifuffukan ba. Amma za a cigaba da tsare a gidan yari kafin ya samu beli.

Williams Tijjani ya roki kotu ta tsare Kayode har zuwa lokacin da za a saurari shari’ar bada belinsa. Lauyan wanda ake tuhuman, bai ja a kan wannan ba.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan banki sun hadu da fushin doka bayan sun sace kudin mamaci a bankinsu

Emeka Okpoku (SAN) ya bukaci Alkali ya sa rana domin a nemi belin Kayode. Mai shari’a, Tijjani Ringim ya daga shari’a zuwa ranar 11 ga watan Agusta, 2021.

An dauke mahaifin shugaban majalisar dokoki

A jihar Zamfara, masu garkuwa da mutane sun addabi karamar hukumar Zurmi a 'yan kwanain nan, har ta kai sun dauke ‘tanuwan shugaban majalisar dokoki.

'Yan bindiga sun dauke dattijon da ya haifi shugaban majalisar jihar Zamfara, Alhaji Nasiru Muazu Magarya, da kishiyar mahaifiyarsa, da wasu mutane biyar.

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel