Da duminsa: Mutum 1 ya sheka lahira yayin da 'yan fashi suka kai farmaki bankuna 2
- Wasu miyagun 'yan fashi sun kai mugun farmaki a bankuna biyu dake Iree a karamar hukumar Boripe ta jihar Osun
- 'Yan fashin sun kutsa garin dake yankin kudu maso yamma na jihar da yammacin Alhamis, 5 ga watan Augusta inda suka dinga harbi
- SP Yemisi Opalola, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Osun, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace an kashe mutum 1
Osun - Wani rahoto da ya fito daga jaridar The Nation ya bayyana yadda wasu miyagun 'yan fashi da makami a ranar Alhamis, 5 ga Augusta suka kai farmaki wasu bankuna biyu dake Iree, karamar hukumar Boripe ta jihar Osun.
Jaridar ta kara da cewa an sheke mutum daya yayin da 'yan fashin suka kutsa yankin wurin karfe 3 da minti hamsin na rana kuma suka dinga harbe-harbe.
Me ganau suka ce akan aukuwar lamarin?
Wani mazaunin yankin mai suna Fisayo ya ce 'yan fashin sun dinga harbe-harbe domin tsorata jama'a kafin su shiga bankunan.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Osun, SP Yemisi Opalola ya tabbatar da aukuwar lamarin.
SP Yemisi Opalola ya kara tabbatar da cewa tuni aka tura jami'an tsaro inda lamarin ya faru.
Amma kamar yadda The Cable ta ruwaito, an kashe mutum biyu ne yayin da 'yan bindiga suka kaiwa bankuna biyun farmaki.
Amma kamar yadda wallafar Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito, wani ganau ba jiyau ba yace an sheke mutum biyu kuma miyagun sun yi awon gaba da makuden kudade.
Matasan PDP sun yi wa Jega wankin babban bargo kan kwatanta APC da PDP
Matasan jam’iyyar PDP sun yi wa tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, wankin babban bargo akan alakanta jam’iyyarsu da APC, Daily Trust ta wallafa.
Shugabannin jam’iyyar adawar ta PDP sun koka da Jega akan rashin nunawa ‘yan Najeriya gaskiya saboda suna zarginsa da zama daya daga cikin wadanda suka dakatar da cigaban Najeriya tun 2015.
A wata takarda wacce shugaban jam’iyyar na kasa, Salaudeen A. Lukman ya sanya hannu, matasan PDP sun nuna takaicin su akan maganganun da tsohon shugaban INEC din yayi a BBC akan zargin ko dai da gangan yake yi don ya rudar da jama’a ko kuma salo ne na tallata sabuwar jam’iyyarsa.
Asali: Legit.ng