Wadanda suka dauke Mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Bayelsa sun ce a biya fansar N500m
- Madam Betinah Benson ta fada hannun masu garkuwa da mutane a jihar Bayelsa
- Tsohuwar mahaifiya ce a wurin sakataren gwamnatin Bayelsa. Kombowei Benson
- ‘Yan bindiga na neman Naira miliyan 500 kafin su saki dattijuwar mai shekara 80
Bayelsa – Ana zargin masu garkuwa da mutane sun yi awon-gaba da wata tsohuwa, Betinah Benson, mahaifiyar sakataren gwamnatin jihar Bayelsa.
An lafta N500m a kan Madam Betinah Benson
The Nation ta ce Madam Betinah Benson mai shekara 80 a Duniya ita ce mahaifiyar Dr. Kombowei Benson
‘Yan bindigan da suka tsare wannan tsohuwa sun bukaci iyalanta su fito da Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansa, idan suna sha’awar sake ganinta.
Jaridar ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar a ranar Juma’a, 6 ga watan Agusta, 2021. Kawo yanzu dai makonni biyu kenan babu labarin Betinah Benson.
Tari Ajanami ya na hannun masu garkuwa da mutane
Har yau, wasu gungun ‘yan bindiga sun bukaci a biya Naira miliyan 200 domin a saki shugaban babban gidan rawan nan na Club 64, watau Tari Ajanami.
Kamar yadda mu ka samu labari, jami’an tsaro suna zargin ‘yan bindigan da suka yi garkuwa da Madam Betinah Benson ne suke tsare da Mista Ajanami.
Da aka nemi jin ta bakin mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sandan Bayelsa, Asinim Butswat, bai iya tabbatar wa ‘yan jarida da wannan labari ba.
Amma wani daga cikin ‘yanuwan Tari Ajanami, ya tabbatar da cewa an dauke ‘danuwan na su.
“Na yi mamaki sosai da na ji cewa suna neman Naira miliyan 200. Ina fata tare da addu’ar su fito da ‘danuwanmu ba tare da sun yi masa wani lahani ba.”
Ba yau aka fara awon gaba da Betinah Benson ba
Jaridar Punch ta ce an dauke mahaifiyar sakataren gwamnatin ne a gidan ta da ke tsohuwar unguwar ‘yan majalisu da ke babban birnin Bayelsa, Yenagoa.
A 2013, an sace wannan mata a gidan ta da ke unguwar Korokorosei a karamar hukumar Ijaw. An kuma taba sace surukar sakataren gwamnatin, Ogboro Orumo.
Kwanakin baya an ji wasu masu garkuwa da mutane sun sace mutane shida da ke zaune a unguwar Tungan-Maje, ƙaramar hukumar Gwagwalada, Abuja.
Hakimin Tungan-Maje, Alhaji Hussaini Barde ya tabbatar da harin, yana mai kira a kawo masu agaji.
Asali: Legit.ng