Kotun Musulunci Ta Ki Amincewa da Bukatar Sheikh Abduljabbar Kan Mukabalar da Aka Yi

Kotun Musulunci Ta Ki Amincewa da Bukatar Sheikh Abduljabbar Kan Mukabalar da Aka Yi

  • Babban alkalin jihar Kano, Mai Shari’a Nura Sagir, ya yi fatali da bukatar sheikh Abduljabbar Kabara
  • Shehin malamin ya nemi kotu ta yi watsi da shawarwarin dake cikin rahoton mukabala da alƙali ya bayar
  • Abduljabbar ya kara nanata cewa ba'a masa adalci ba a wurin mukabalar sannan ba'a bashi lokaci ba

Kano:- Babbar Kotun jihar Kano ta yi fatali da bukatar malam Abduljabbar na jingine sakamako da shawarwarin alkalin mukabalar da ta gudana tsakaninsa da malaman Kano.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa a ranar 10 ga watan Yuli wasu malamai suka gwabza mukabala da Abduljabbar kan wasu maganganu da yake yi a karatunsa.

Mukabalar wadda gwamnatin jihar Kano ta shirya ta gudana bisa amincewar Abduljabbar kuma kan wasu maganganu da yake a karatunsa da malaman Kano ke ganin batanci ne ga Manzon Allah (SAW).

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Kotun Musulunci Ta Ki Amincewa da Bukatar Sheikh Abduljabbar Kan Mukabala Hoto: rfi.fr
Asali: UGC

Wace shawara alƙalin ya baiwa gwamnatin Kano?

Alkalin mukabalar, Farfesa Salisu Shehu, ya bayyana cewa shehin malamin ya gaza amsa ko tambaya ɗaya da aka masa, sai zagaye-zagaye yake da maimata cewa babu lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta bayyana dalilin da yasa ba za ta tattauna da 'yan bindiga ba

Alƙalin yace:

"Kowa yaji kuma ya saurara tun da muka fara mukabalar nan har zuwa yanzu da muka kammala malam Abduljabbar bai amsa ko tambaya ɗaya ba daga cikin tambayoyin da aka masa."
"A duk sanda ya amshi abun magana sai ya kama korafin ba lokaci yana kame-kame amma babu cikakkiyar amsa.

Farfesa Shehu ya mika sakamakon mukabalar ga wakilin gwamnati, sannan ya shawarci gwamnatin Kano ta ɗauki matakin da ya dace a kan Abduljabbar.

Shin Abduljabbar ya amince da shan kaye?

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi watsi da sakamakon mukabalar inda ya yi zargin cewa ba'a masa adalci ba.

Malamin ya kuma yi zargin cewa ba'a ba shi isasshen lokacin amsa tambayoyin da aka masa ba.

Abduljabbar ya bukaci jingine mukabala

Bayan hakane, malamin ya shigar da bukata gaban babbar kotun jihar Kano, inda ya nemi ta yi fatali da shawarwarin da alƙali ya bayar a cikin rahoton mukabalar.

Kara karanta wannan

Karin yan Boko Haram 19 sun mika wuya ga jami'an Sojoji a Borno

Sai dai kuma alƙalin kotun kuma babban alƙalin jihar, Mai Shari’a Nura Sagir, ya yi watsi da bukatar malam Abduljabbar, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Kungiyar IPOB da Yarbawa Dake Son Ballewa

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano , yace kokarin ballewa daga ƙasa ba shine hanyar warware ƙalubalen da muke fama da shi ba.

Ganduje ya faɗi haka ne a wurin wata Lakca da jam'iyyar APC ta shirya a Abuja , kamar yadda the cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel