Miyagu sun kona motoci kurmus, sun kashe Bayin Allah a Jos bayan rikicin da suka barke

Miyagu sun kona motoci kurmus, sun kashe Bayin Allah a Jos bayan rikicin da suka barke

  • A jiya Miyayu suka tare hanyar zuwa Gada-Biyu a garin Jos da ke Jihar Filato
  • An rika jin karar bindigogi a yankin, aka kona wasu manyan motoci har biyu
  • Mutane biyu ake tunani sun mutu a wannan sabon harin da aka kai cikin dare

Jos - Zuwa yammacin ranar Talata, 3 ga watan Agusta, 2021, mutane akalla biyu suka bakunci barzahu a sakamakon wani tashin-tashina a jihar Filato.

A jiyan wasu ‘yan iskan gari suka tare babban titin zuwa Gada-Biyu a garin Jos, babban jihar Filato.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa wadannan ‘yan iskan gari sun banka wa manyan motoci biyu wuta a daren Laraban nan.

Wadannan motoci sun kone kurmus, sannan miyagun mutanen suka shiga tare matafiyan da su ka biyo ta hanyar zuwa garin Gada-Biu, su na kai masu hari.

Me ya jawo wannan tashin-tashina?

Rahoton ya bayyana cewa babu mamaki ‘yan iskan sun yi wannan danyen aiki ne a sakamakon rikicin da ake yi tsakanin makiyaya da kuma mutanen Irigwe.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin jama'an gari da yan Shi'a a jihar Kano

A dalilin wannan sabani da aka samu, an hallaka mutane da dama a jihar Filato a makon da ya wuce.

Gwamna Simon Lalong
Gwamna Simon Lalong da abokan aikinsa Hoto: theeagleonline.com
Asali: UGC

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Filato, Edward Egbuka, yace an kashe mutane 17, kuma an kona gina-gine fiye da 80 a rikicin da ya barke a Bassa da Riyom.

Mazauna sun tsere sun bar 'ya 'ya da matansu

Jaridar Sun ta ce an fara jin karan harbin bindigogi ne da kimanin karfe 9:30 na dare a yankin. Bidiyoyi sun nuna yadda aka kona wasu motocin Bayin Allah.

Baya ga haka an banka wuta ga wasu tayoyi a kan babban titin na Goodluck Jonathan, yayin da mafi yawan mazauna yankin suka tsere domin ceton ransu.

Rahoton da Sun ta fitar ya ce an bar kananan yara da mata carko-carko bayan an fara wannan harbe-harbe, ana kona dukiyoyi, ana kuma tare masu bin titin.

An yi rin haka a baya

Kara karanta wannan

Ayi hattara, sabon samufurin COVID-19 ya shiga Abuja, da wasu Jihohi 7 inji Gwamnatin Tarayya

Kwanakin baya an ji 'yan bindga sun kai wa motar wani mai rike da sarautar gargajiya a karamar hukumar Bassa, jihar Filato, Daniel Chega hari a kan hanya.

Mai martaban ya gamu da harin 'yan bindiga ne bayan ya tashi daga wani zama da aka yi da nufin samun zaman lafiya, an taki Chega sa'a ya tsira a harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng