Nasara daga Allah: 'Yan Boko Haram 88 sun mika wuya da makamansu ga sojojin Najeriya

Nasara daga Allah: 'Yan Boko Haram 88 sun mika wuya da makamansu ga sojojin Najeriya

  • Sakamakon cigaba da bude wa ‘yan Boko Haram wuta da rundunar soji ta Operation Hadin Kai suke yi, sun fara mika wuya
  • Manyan mayakan boko Haram maza 19, mata 19 da yara 49 daga kauyen Njimia da kewaye sun mika wuya ga sojoji
  • Mayakan sun koka da cewa yanzu haka zaman cikin dajin ya gagaresu kullum a cikin tashin hankali da fargaba suke

Njimia, Borno - Sakamakon bude wutar da Operation Hadin Kai suke yi wa ‘yan Boko Haram, tuni ‘yan ta’addan da iyalansu suka fara mika wuya ga sojoji suna zubar da makamansu, prnigeria ta wallafa.

‘Yan Boko Haram wadanda suka zagaye dajin Sambisa bayan sun ji aman bama-bamai daga sojin sama dana kasa sun nufi sansanin sojoji na Forward Operational Base (FOB) dake Banki Junction/BOCOBS a Bama dake jihar Borno a ranar 2 ga watan Augustan 2021.

Nasara daga Allah: 'Yan Boko Haram 88 sun mika wuya da makamansu ga sojojin Najeriya
Nasara daga Allah: 'Yan Boko Haram 88 sun mika wuya da makamansu ga sojojin Najeriya. Hoto daga prnigeria.com
Asali: UGC

‘Yan ta’addan sun yadda makamansu sannan sun mika wuya, cikinsu akwai mayaka maza manya guda 19, mata 19 da yara 49 daga kauyen Njimia da kewaye.

Kara karanta wannan

Daya daga cikin 'yammatan Chibok da mijinta dan Boko Haram sun mika wuya ga sojoji

Amma me yasa suka mika wuya?

‘Yan Boko Haram din sun koka bisa halin rashin kwanciyar hankalin da damuwar da suke ciki a dajin.

Sun mika makamansu wadanda suka hada da bindigogi Ak 46 guda 8, wani injin hada bindigogi na GPMG, Fabrique Nationals Rifles guda 2, bindigar yaki daya, karamar bindiga daya, Special ammunition na 7.62mm guda 89, carbin harsasai na 12.7mm gud 89, carbin harsasai na NATO guda 66 da sauran miyagun makamai.

An samu bama-bamai a hannunsu, rigar abu mai fashewa, wayoyi guda 6, ashanoni da sauran karikitai har da kudi naira 55,000, prnigeria ta ruwaito.

Yanzu haka ‘yan ta’addan da iyalansu suna hannun jami’an tsaro ana kara bincike akansu sannan yaran kuma ana yi musu allurar polio.

Daya daga cikin 'yammatan Chibok da mijinta dan Boko Haram sun mika wuya ga sojoji

Tsohuwar dalibar GSS Chibok dake jihar Borno da mijinta, dan Boko Haram sun mika wuyansu ga sojojin Najeriya kamar yadda PRNigeria ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Bakare: Abokin tafiyar Buhari ya ba shi shawarar abin yi, ya daina sukar shugabannin baya

Dalibar tana daya daga cikin dalibai 200 da ‘yan Boko Haram aka sata a ranar 14 ga watan Afirilun 2014.

Duk da dai sojojin basu sanar da sunan dalibar ba, amma an tabbatar da yadda ita da mijinta suka sanar da tubansu daga kungiyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel