Gaskiya na tafka babban kuskure - Bill Gates ya ciza yatsa bayan rabuwa da Mai dakinsa

Gaskiya na tafka babban kuskure - Bill Gates ya ciza yatsa bayan rabuwa da Mai dakinsa

  • Bill Gates ya yi maganar farko da ‘yan jarida bayan ya rabu da Mai dakinsa
  • Attajirin ya ce ya tafka babban kuskure da ya rika zama da Jeffrey Epstein
  • Gates ya bayyana cewa mutuwar aure ba za ta raba sa da Melinda French ba

Amurka - Babban ‘dan kasuwan Duniya, Bill Gates, ya yarda ya yi kuskuren yin hulda da Jeffrey Epstein, wani gawurtaccen mutumin banza a Amurka.

Da yake magana da CNN a karon farko tun da ya saki mai dakinsa, ya ce ya yi nadamar rabu wa da uwar ‘ya ‘yansa, haka zalika alakarsa da Jeffrey Epstein.

Bill Gates ya na da-na-sanin zama da Jeffrey Epstein

“Abin takaici ne sosai, karshe bai yi kyau ba; Melinda mutumiyar kirki ce, kuma a ce alakarmu ya zo karshe, abin takaici ne a rayuwata.”
“Na zauna da shi sosai mun ci abinci, da nufin abin da ya ce na taimaka wa Duniya da makudan biliyoyi da nufin bunkasa harkar lafiya.”

Kara karanta wannan

Bakare: Abokin tafiyar Buhari ya ba shi shawarar abin yi, ya daina sukar shugabannin baya

“Da ya bayyana kamar abin ba gaskiya ba ne, sai dangantakar mu ta zo karshe. Amma babban kuskure ne kashe lokaci na da shi.”

Mutumin da ya kafa kamfanin na Microsoft ya ce ya yi nadamar yarda da mutum irin Epstein, ya ce ba wannan ne karon farko da ya yi wannan kuskuren ba.

Bill Gates
Bill Gates da Melinda French Gates Hoto: www.bloomberg.com
Asali: UGC

Amma har yanzu mu na tare - Bill Gates

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin, dattijon ya ce duk da auren shi da Melinda ya mutu kuma sun rabu, za su cigaba da aiki tare a gidauniyar da suka kafa

“Mun ji dadin aiki a tare. Za mu cigaba da alakarmu, mu zauna da shugabanni domin karfafa kungiyarmu, hakan zai fi kyau ga gidauniyarmu.”

A ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, 2021, Bill Gates da Melinda French Gates suka tabbatar da cewa aurensu ya rabu bayan shekara da shekaru suna tare.

Kara karanta wannan

Allah Zai Wanke Abba Kyari, Hassada Wasu Ƴan Sanda Ke Masa: Ahmad Isah, Mai Gabatar Da Shirin ‘Brekete Family’

Da aka shiga kotu, Alkali ya amince da rabuwar auren hamshakin attajirin da kuma matarsa Melinda French Gates bayan sun bukaci a katse igiyar alakarsu.

A baya jaridu irinsu New York Times da WSJ sun rahoto cewa alakar Bill Gates da Jeffrey Epstein ya na cikin abin da ya kashe masa aure da Melinda French.

Asali: Legit.ng

Online view pixel