Da Duminsa: Kallo Ya Koma Sama Yayin da Wani Gwamna Ya Dira Dakin Taron Dattijan PDP

Da Duminsa: Kallo Ya Koma Sama Yayin da Wani Gwamna Ya Dira Dakin Taron Dattijan PDP

  • Mambobin kwamitin amintattu (BoT) sun fara taro kan yadda za'a magance matsalolin dake faruwa a jam'iyyar PDP
  • Gwamna Wike na jihar Rivers ya shiga dakin taron ba zato ba tsammani yayin da shugaban PDP ke jawabin buɗewa
  • Gwamnoni basa cikin BoT kuma basu halartar taronsu, sai dai babu masaniyar ko an gayyaci Wike

FCT Abuja:- Yayin da ake cikin taron dattijan jam'iyyar PDP domin lalubo hanyar warware rikicin da ya kunno kai, anga gwamnan Rivers Nyesom Wike, ya shiga ɗakin taron ba zato ba tsammani.

Vanguard ta ruwaito cewa mutane da dama sunga isar Wike sakateriyar yayin da ake rade-radin cewa yana cikin waɗanda suka matsa a tunbuke shugaban PDP na yanzu, Uche Secondus.

Taron dai na mambobin kwamitin amintattu ne wato BoT kuma sun kira taron ne domin tattaunawa kan abubuwan dake faruwa a cikin jam'iyyar PDP.

Shugaban PDP, Uche Secondus da Gwamna Wike na jihar Rivers
Da Duminsa: Kallo Ya Koma Sama Yayin da Wani Gwamna Ya Dira Dakin Taron Dattijan PDP Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shin gwamnoni na cikin BoT?

The nation ra tuwaito cewa shigar gwamna Wike ba tare da tsammani ba ya jawo rudani domin gwamnoni basu cikin mambobin BoT kuma basu halartar taron BoT.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam'iyyar APC, mambobin majalisar zartarwa duk sun yi murabus, sun koma PDP

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan Rivers ɗin ya tattaka zuwa ciki dakin taron kwamitin zartarwa (NEC) inda ake gudanar da taron a dai-dai lokacin da Secondus yake jawabin buɗewa.

Mahalarta taron sun koma kallon gwamnan wanda ya nemi wurin zama cikin mahalarta taron ya zauna.

An gayyaci Wike zuwa taron ne?

Sai dai har zuwa yanzun babu wani cikakken bayani kan cewa ko mambobin BoT ne suka gayyaci gwamnan.

Taron mambobin kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP dake gudana yanzun haka ya samu halartar manyan ƙusoshin jam'iyyar waɗanda suka haɗa da tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark.

Sauran sun haɗa da Adolphus Wagbara, Sanata Abdul Ningi, da kuma shugaban kwamitin, Sanata Walid Jibrin da sauransu.

Rikicin APC a Zamfara

A ɗaya ɓangaren kuma jam'iyya mai mulki na fama da nata rikicin a jihar Zamfara inda ake ta kace-nace game da kasafta kujerun shugabancin APC a jihar da kuma mukaman gwamnati.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Zamfara: Mun Fi Karfin Kashi 30, Yari Ya Maida Martani Ga Gwamna Matawalle

Tsojon gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari, yayi fatali da kashi 30 na mukaman da gwamnan Zamfara ya basu.

A cewarsa sune ruhin APC a jihar idan ba'a ba su kaso mafi tsoka ba to fa sai dai a raba dai-dai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel