Sojoji sun yiwa Boko Haram lugude, sun samo makamai, maganin karfin maza da littafin hada bam

Sojoji sun yiwa Boko Haram lugude, sun samo makamai, maganin karfin maza da littafin hada bam

  • Sojojin Najeriya sun yi wa mayakan ta'addanci na Boko Haram lugude a Gubio dake jihar Borno
  • Sun samo miyagun makamai, magungunan karfin maza tare da wani littafin yadda ake hada bam
  • An samu nasarar aikin ne sakamakon hadin guiwar dakarun sojin sama da na kasa na Najeriya

Gubio, Borno - Mayakan Boko Haram da na ISWAP a ranar Talata sun sha ruwan wuta a hannun dakarun sojin Najeriya wadanda suka shirya gagarumin aikin kakkabo miyagu.

A wannan samamen, dakarun sun tarwatsa motocin yaki hudu na 'yan ta'addan a Gubio dake jihar Borno.

Jirgin sojin saman Najeriya ya dinga sakin wuta ta sama yayin da sojin kasa suka bi 'yan ta'addan suna shekewa.

Sojoji sun yi Boko Haram lugude, sun samo makamai, maganin karfin maza da littafin hada bam
Sojoji sun yi Boko Haram lugude, sun samo makamai, maganin karfin maza da littafin hada bam. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda Emergency Digest ta wallafa, Dakarun sojin kasa suna tsaka da ragargazar miyagun a Gubio lokacin da jirgin yaki ya garzaya kamar yadda aka umarcesa domin bada taimako.

Me aka samo daga wurin 'yan ta'addan?

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun cafke miyagun kwayoyin da aka shigowa da 'yan bindiga

Manyan bindigogi, harsasai, rigunan yaki, jarkoki, wiwi, maganin karfin maza da kuma wani littafi na yadda ake hada bama-bamai na daga cikin abubuwan da aka samo.

Hakazalika, bayan hango miyagun 'yan ta'addan a Sambisa wuraren Parisu zuwa Njimiya, wani jirgin yakin sojin sama ya bi su inda ya murkushesu.

Mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya ce samamen da suka kai ta jiragen yaki duk an samu nasara.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Christopher Musa ya jinjinawa dakarun sojin a kan gwarzantakar da suka nuna, Emergencydigest ta ruwaito.

Bidiyon sojojin Najeriya suna raka yara makaranta a yankin arewa maso gabas

Bidiyon sojoji suna raka wasu daliban makaranta zuwa makaranta a arewa maso gabas a Najeriya ya taba zukatan mutane da dama.

Yanzu ‘yan bindiga sun fi harin daliban makaranta don har yanzu akwai sauran dalibai a hannun masu garkuwa da mutane bayan sun sacesu daga makarantunsu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sunfi IPOB da Igboho hatsari - Tsohon Sanata

Sakamakon cigaba da satar dalibai, jihohi da dama suka rufe makarantun sakandare na wani lokaci, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Don samar da kariya ga dalibai, sojojin Najeriya sunyi tsiri tsayawa kusa da makarantu amma duk da haka wasu makarantun babu tsaro.

A wani bidiyo wanda ya bayyana babu dadewa an ga yadda sojoji suke raka yara makaranta don tabbatar da isarsu lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel