An Cafke Wani Dalibin Jami'a Ya Yi Shigar Mata Ya Zauna Jarabawar Budurwarsa

An Cafke Wani Dalibin Jami'a Ya Yi Shigar Mata Ya Zauna Jarabawar Budurwarsa

  • Dubun wani ɗalibin jami'a ta cika inda aka kama shi a ɗakin jarabawa yayi shigar mata a ƙasar Senegal
  • Rahoto ya nuna cewa ɗalibin ya yi haka ne domin farantawa budurwarsa rai ya zauna mata jarabawa
  • A halin yanzun an kama shi da budurwar tasa kuma an gurfanar da su a gaban mai shari'a

Senegal:- Wani ɗalibin ƙasar Senagal ya shiga hannu bisa zargin ya yi shigar mata kuma ya zauna wa budurwarsa jarabawa, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Lauyan dalibin ne ya bayyana haka kuma yace ita ma budurwar tasa ta shiga hannun dukkan su a zarginsu da aikata zamba cikin aminci.

A halin yanzun saurayi da budurwar tasa an gurfanar da su a gaban kotu a kan karar aikata zamba da kuma haɗa kai don aikata zamba cikin aminci.

An kama wani ɗalibin jami'a yana rubutawa budurwarsa jarabawa da shigar mata
An Cafke Wani Dalibin Jami'a Ya Yi Shigar Mata Ya Zauna Jarabawar Budurwarsa Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Channels ta ruwaito Lauya Serigne Ndiongue yana cewa:

"Gaba ɗaya waɗanda ake zargin suna fuskantar shari'a iri ɗaya domin sun aikata laifi da haɗin kan juna."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fusatattun Daliban Wata Jami'an Sun Toshe Babbar Hanya Saboda Sheke Dan Uwansu

A cewar mai gabatar da kara, Dalibin ya yi tafiya har zuwa tsakiyar birnin Diourbel domin ya rubutwa budurwarsa jarabawa a madadinta.

Hotuna sun watsu a kafafen sada zumunta

Hotunan dake yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ɗalibin ya saka kayan mata masu kalar ja da kuma abun wuya baƙi.

Rahotanni sun bayyana cewa mai kula da ɗakin jarabawa ne ya gano shi a rana ta uku bayan ya fahimci a kwai damuwa a yanayin shigarsa.

Daga nan kuma sai aka mika shi ga jami'an yan sanda domin su gudanar da bincike.

A wani labarin kuma Hotunan Jagoran Jam'iyyar APC Bola Tinubu da Wani Gwamna a Birnin Landan

Jagoran jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya karbi bakuncin gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu a Landan ranar Talata.

Tinubu ya jima baya ƙasar nan, inda ya tsallake muhimman ayyukan jam'iyyarsa ta APC.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyukan Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 18

Asali: Legit.ng

Online view pixel