An Kama Mata Da Miji Da Suka Yi Ƙaryar Garkuwa Da Ƴarsu Don Su Samu Kuɗi Su Biya Bashin Banki Ta Suka Ci

An Kama Mata Da Miji Da Suka Yi Ƙaryar Garkuwa Da Ƴarsu Don Su Samu Kuɗi Su Biya Bashin Banki Ta Suka Ci

  • Yan sanda sun kama iyayen da suka shirya garkuwa da yarsu don biyan bashin banki da suka ci
  • Iyayen sun karbi bashin Naira miliyan 17 ne daga bankin don bunkasa sana'a amma abin ya rushe
  • Majiyoyi sun bayyana cewa yan sandan da ke bincike kan lamarin sun gayyaci iyayen bayan samun bayanan sirri kan cewa suna da hannu a garkuwar

Warri, jihar Delta - Rundunar yan sandan jihar Delta sun kama miji da mata kan yin garkuwa da yarsu mai shekaru 21, Stephanie Solomon Oghenevoke kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A baya dai an ayyana cewa yarinyar ta bace bayan ta bar wurin aiki a Okumagba Estate a Warri, a ranar 19 ga watan Yulin 2021, kuma bata dawo ba.

An Kama Mata Da Miji Da Suka Yi Ƙaryar Garkuwa Da Ƴarsu Don Su Samu Kuɗi Su Biya Bashin Banki Ta Suka Ci
Yan sanda sun kama iyayen da suka shirya garkuwa da yarsu don biyan bashin banki. Hoto: The Punch
Asali: UGC

A cewar The Punch, an kama iyayen a daren ranar Lahadi 1 ga watan Agusta, bayan yan sanda da ke bincike kan lamarin sun samu labarin sirri cewa iyayen ne suka shirya garkuwar da yarsu.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin jama'an gari da yan Shi'a a jihar Kano

Majiyoyi sun shaidawa majiyar Legit.ng cewa yan sandan B-Division, Warri a ranar Litinin da yamma sun gayyaci iyayen Stephanie da ke zane a Olomu Street domin amsa tambayoyi.

Daya daga cikin majiyoyin ya yi zargin cewa Stephanie Solomon, ma'aikataciyar banki da ke Okumagba Estate, Warri, ta taimakawa iyayen ta wurin karbar bashin Naira miliyan 17 daga bankin.

Mene ya sa iyayen karbar bashin bankin?

An gano cewa sun karbi bashin ne domin bunkasa kasuwancinsu amma sai sun samu faduwa a kasuwancin kuma sun gaza buyan bashin har ta kai ga cewa bankin ta fara matsa musu lamba su dawo da bashin.

A cewar rahoton, an gano cewa mata da mijin, a yunkurin nemo kudin da za su biya bashin bankin sun yanke shawarar shirya garkuwa da yarsu.

A halin yanzu dai ba a riga an sako yarinyar da aka ce an yi garkuwar da ita ba a cewar majiyoyi.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe ya ce ba zai iya tabbatar da rahoton ba a lokacin da aka tuntube shi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa asibiti a jihar Zamfara

A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

A wani labarin mai kama da wannan, Jami'an yan sanda na jihar Adamawa sun kama wani mutum mai shekaru 41, Usman Hammawa, bisa zarginsa da yi wa matarsa mai shekaru 36 duka, saboda N1,000 har sai da ta mutu.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin Rabiyatu Usman da mijinta ne bayan ta bukaci ya biya ta bashin N1,000 da ya karba daga hannunta.

Usman Hammawa, mazaunin yankin Jada a karamar hukumar Ganye ta jihar Adamawa, ya halaka matarsa ne ta hanyar buga kanta da bango, hakan yasa ta fadi sumammiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel