Da Ɗumi-Ɗumi: An Bindige Masu Garkuwa Har Lahira Yayin Karɓar Kuɗin Fansa a Taraba

Da Ɗumi-Ɗumi: An Bindige Masu Garkuwa Har Lahira Yayin Karɓar Kuɗin Fansa a Taraba

  • Yan banga sun bindige wasu masu garkuwa da mutane a yayin da suka zo karbar kudin fansa
  • Masu garkuwar sun sace wani dattijo ne kuma suka umurci yan uwan su kawo kudin domin fansarsa
  • Sai dai kafin su tafi kai kudin, yan uwan dattijon sun sanar da yan banga wanda su kuma suka yi wa masu garkuwar kwantar bauna suka bindige su

Gassol, Jihar Taraba - An bindige wasu masu garkuwa da mutane biyu har lahira yayin da suka zo karbar kudin fansa a garin Sabongida da ke karamar hukumar Gassol na jihar Taraba.

Daily Trust ta gano cewa wadanda ake zargin sun sace wani dattijo ne mai suna Alhaji Gambo.

Da Ɗumi-Ɗumi: An Bindige Masu Garkuwa Har Lahira Yayin Karɓar Kuɗin Fansa a Taraba
Da Ɗumi-Ɗumi: An Bindige Masu Garkuwa Har Lahira Yayin Karɓar Kuɗin Fansa a Taraba
Asali: Original

Wadanda ake zargi da garkuwar masu suna Sani da Musa sun umurci iyalan wanda suka sace din su kawo kudin fansar zuwa wani wuri.

Yadda yan bangan suka shirya wa masu garkuwar harin kwantar bauna

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Kaduna daga 'yan bindiga

Daily Trust ta ruwaito cewa an sanar da yan banga da ke yankin kuma suka tafi wurin domin yi wa masu garkuwar kwantar bauna.

Masu garkuwan sun tawo da makamansu, amma ba su san cewa yan bangan suna wurin ba kuma suka bindige su a lokacin da suke kwashe kudaden.

An ceto dattijon da suka kawo shi wurin da za su karba kudin fansa.

Wata majiya ta bayyana cewa masu garkuwar da aka kashe sun halaka mutane da dama a kauyukan Borno-Korokoro,Tella, Sabongida, Dananacha da wasu kauyuka da ke hanyar Jalingo zuwa Wukari duk a jihar Taraba.

Rundunar yan sandan Taraba ta tabbatarda kashe masu garkuwar

Mai magana da yawun yan sandan jihar Taraba, ASP Abdullahi Usman, ya tabbatar da kashe masu garkuwan amma bai yi karin bayani ba.

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon wani mutumi yanawa yan jami'a ruwan kudi daga sama ya jawo cece-kuce

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164