Bidiyon wani mutumi yanawa yan jami'a ruwan kudi daga sama ya jawo cece-kuce

Bidiyon wani mutumi yanawa yan jami'a ruwan kudi daga sama ya jawo cece-kuce

  • Daliban jami'a sun yi wawason kudi a jami'ar arzikin man fetur
  • Wannan dabi'a ya fara zama ruwan dare a Najeriya
  • Gwamnati ta haramta likin kudi tare da takashi a kasa

Delta - Wani bidiyo daya watsu a kafar zata zumunta ya sanya mutane cikin mamaki

A bidiyon wanda @instablog9ja, ya wallafa, an ga wani mutumi yana watso kudi ga daliban jami'ar arzikin man fetur ta jihar Delta daga sama su kuma daliban suka bazama suna kwashewa daga kasa.

Daliban basu damu da wadanda suke kallansu ta sama ba.

Idan baka lura da kyau ba zaka sha ruwan sama na kudi ake yi yadda shima mutumin ya kware wurin watso kudin, amma kuma ba'a bayyana dalilin shagalin da ya janyo wannan ruwan kudin ba.

Bidiyon wani mutumi yanawa yan jami'a ruwan kudi daga sama ya jawo cece-kuce
Bidiyon wani mutumi yanawa yan jami'a ruwan kudi daga sama ya jawo cece-kuce Credit: @instabloggja Source: Instagram
Asali: Instagram

Ga abinda mutane suka ce

@sis.ekwutos yace:

"Kai! Dan Allah wannan mutanan su karaso makarantanmu mana..Ghana must go kawai zan kwashe kudin aciki in tafi abina, kawai zanje na siya buhun garri da siga kafin EFCC suzo da wahalarsu."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sunfi IPOB da Igboho hatsari - Tsohon Sanata

@iteegoigbo yace:

"Abokina ya gama a wannan makarantar. Kawu yanzu aikin banki yake yi. baiga aikin mai da zaiyi ba."

@miss_social20 cewa yayi:

"Ku kyale su su diba, Abokina ka diba, saboda ka samu ka ci abinci...kana bukatar karfi domin zama manyan gobe.

" @ziggys_kiddies yace:

"Lallai kam. Waye yake zubo wannan kudaden??? EFCC na nan zuwa gareku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel