Yajin Aikin ASUU: FG Ta Bayyana Yadda Ganawarta da ASUU Ta Kasance, Zata Saki Biliyan N30bn

Yajin Aikin ASUU: FG Ta Bayyana Yadda Ganawarta da ASUU Ta Kasance, Zata Saki Biliyan N30bn

  • Gwamnatin tarayya ta nuna gamsuwarta game da taron da ya gudana tsakaninta da ASUU
  • Ministan kwadugo, Chris Ngige, ya bayyana taron na su a matsayin wanda aka ci nasara
  • Shugaban ASUU ta kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, yace zasu yi taro da sauran mambobinsu domin duba abun yi

FCT Abuja:- Gwamnatin tarayya ta bayyana taron ta da kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) domin duba yarjejeniyar gudanarwa (MoA) a matsayin wanda aka samu nasara, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, ministan kwadugo, Chris Ngige, yace taron ya tattauna muhimman abubuwa 7.

Ministan ya bayyana cewa kowane ɓangare ya nuna gamsuwarsa da matakin aiwatarwa da ake ciki yanzun haka.

Taron FG da ASUU ranar 2 ga watan Agusta
Yajin Aikin ASUU: FG Ta Bayyana Yadda Ganawarta da ASUU Ta Kasance, Zata Saki Biliyan N30bn Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace wasu daga cikin abubuwan da aka amince da su a MoA kusan an kammala aiwatar da su kashi dari bisa ɗari.

Shin an aiwatar da tsarin biyan albashi na UTAS?

Ministan ya kara da cewa an umarci hukumar NITDA da ta gudanar da bincike kan sabon tsarin biyan albashi na UTAS da kungiyar ASUU ta gabatar.

Kara karanta wannan

A yanzu kam manufar mu ita ce sama wa 'yan Najeriya aiki, in ji Gwamnatin Buhari

Wanda a cewarsa idan aka samu nasara zai magance ƙalubalen da malaman ke fuskanta a ɓangaren biyan su albashinsu.

Dakta Ngige yace gwamnati ta riga ta fitad da kuɗi biliyan N30bn na farfado da jami'o'i kamar yadda aka amince a MoA tun a watan Janairu.

Channels tv ta ruwaito ministan na cewa:

"A halin yanzun kuɗin na babban bankin Najeriya (CBN) yayin da ake jiran kammala rahoton bincike na kwamitin gudanarwa dangane da kuɗin da aka fitar a baya."
"Bayan kuɗin alawus biliyan N40bn da gwamnati ta biya, yanzun an saka alawus ɗin malaman na 2021 kimanin biliyan N22bn a cikin karin kasafin kudi kuma ba da jimawa ba za'a sake su."

Wane mataki ASUU zata ɗauka?

A bangaresa, shugaban ASUU na ƙasa, farfesa Emmanuel Osodeke, ya nuna gamsuwarsa game da abinda taron ya kunsa.

Sannan ya yi alkawarin kai dukkan sakamakon taron gaban mambobin kungiyar domin yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Bayan dakatar da Abba Kyari, IGP ya gargadi sauran jam'ian 'yan sandan Najeriya

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana ra'ayinsa na tsarin mulkin karba-karba

Yayin da zaɓen 2023 ke kara gabatowa, gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi kira da aiwatar da mulkin karba-karba domin kowane yanki ya amfana.

Wan nan na zuwa ne yayin da ake samun karuwar neman a kai wa kudanci mulkin kasar nan a babban zaɓen dake tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel