An hana mu ganin Nnamdi Kanu, Lauyan shugaban IPOB ya koka

An hana mu ganin Nnamdi Kanu, Lauyan shugaban IPOB ya koka

  • Daya daga cikin lauyoyin Nnamdi Kanu ya ce an hanasu ganin shugaban IPOB din
  • Dama Kanu yana tsare ne a hannun SSS dake Abuja a bisa umarnin kotu
  • A cewar lauyansa, SSS ta hana su ganinsa a ranar Alhamis duk da kotu ta basu damar hakan

FCT, Abuja - Daya daga cikin lauyoyin Nnamdi Kanu ya ce an hanasu ganin shugaban IPOB. Kanu wanda yanzu haka yana hannun SSS a Abuja bisa umarnin kotu, Premiumtimes ta wallafa.

Lauyansa, Aloy Ejimaker ya ce a ranar Alhamis sun hana shi da sauran lauyoyin Kanu biyu daga ganinsa duk da kotu ta basu damar ganinsa duk wata Litinin da Alhamis.

KU KARANTA: Hotunan Ango Yusuf Buhari da amarya Zahra Bayero yayin wasan Polon bikinsu

An hana mu ganin Nnamdi Kanu, Lauyan shugaban IPOB ya koka
An hana mu ganin Nnamdi Kanu, Lauyan shugaban IPOB ya koka. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Rick Ross: Mawakin gambara da ya mallaki motoci 100 na alfarma, bashi da lasisin tuki

Abinda ya faru yayin da muka ziyarci Kanu

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Sheke Fitaccen mai Satar Jama'a da ya Saci Mahaifinsa ya Karba N4m na Fansa

A cewarsa a lokacin da shi da sauran lauyoyin suka kai masa ziyara inda aka tsare shi, sun yi matukar mamakin yadda jami’an tsaron suka murje ido suka hanasu ganin shi duk da sun san dalilinsu na zuwa.

Na rubuta matsalar da take addabarmu a halin yanzu wacce nakeso a kai ta ga DG na SSS don kada a mayar da ita kamar takardar da ake watsawa a shara.
Don haka mun koma ofishinmu muka shirya ta musamman muka kawo. Sun amshi takardar a hannunmu. Muna wurin tun wuraren 3:30pm har tsawon sa’a daya da rabi muna jiran su bamu damar ganin Kanu.
Sun ce mu jirasu a wurin da ake jiran mutane. Bayan mintuna kadan suka dawo suka ce sun kai takardar ciki don haka mu tafi mu jira a amince, a tabbatar kuma an gayyacemu tukunna,” a cewar Ejimakor.

Har a halin yanzu, mai magana da yawun hukumar tsaron ta farin kaya, Peter Afunanya, bai amsa kira da sakon kar ta kwanan da aka tura masa ba, Premium time ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma

'Yan bindiga sun kutsa babban asibiti a Zamfara

Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kutsa babban asibiti gwamnati dake Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a ranar Juma'a.

Daily Trust ta tattaro cewa miyagun sun yi awon gaba da wata ma'aikaciyar jinya da kuma wata mai jinyar mara lafiya.

Mazauna yankin sun sanar da cewa bayan 'yan bindigan sun shiga asibitin, 'yan bindigan sun fara neman likita ko ma'aikatan jinya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel