Likitoci a Najeriya zasu tsunduma yajin aiki ranar Litinin

Likitoci a Najeriya zasu tsunduma yajin aiki ranar Litinin

  • Kungiyar likitoci zasu shiga yajin aiki ranar 2 ga watan Agusta
  • Wannan umurni ya biyo bayan taron majalisar zartarwa ne a Jihar Abia
  • Shugaban kungiyar Dr Okhuaihesuyi Uyilawa ya bayyana cewa an umurci mambobin dasu fara yajin aikin sai baba ta gani

Kungiyar likitoci a kasar nan (NARD) ta umurci mambobinta dasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani ranar Litinin, 2 ga watan Agusta.

An bada wannan umurnin ne ranar Asabar a karshen wani taron majalisar zartarwa (NEC) wanda aka gudanar a Umuahia, babban birnin jihar Abia kamar yadda Channels ta ruwaito.

Da yake yiwa yan jarida bayani a karshen taron, Shugaban kungiyar, Dr Okhuaihesuyi Uyilawa ya bayyana cewa an umurci mambobin dasu fara yajin aikin sai baba ta gani.

Yace:

"Zamu fara yajin aikin sai baba ta gani a ranar Litinin, 2 ga watan Agustan 2021. Zaku iya tunawa munyi gargadin shiga yajin aikin ranar 31 ga watan Maris 2021 sannan muka sake nanatawa a ranar 9 ga watan Afrilu, saidai tun lokacin ba'a biyan kananan likitoci albashinsu yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Ku mutsike dukkan masu safarar miyagun kwayoyi, Marwa ga jami'an da aka karawa girma

"Mun samu matsala da rashin biyan albashi akan lokaci kuma a bisa gargadin da muka bada, munce ya kamata a dawo biya ta manhajar IPPS."

Da Dumi-Dumi- Likitoci zasu tsunduma yajin aiki ranar Litinin
Da Dumi-Dumi- Likitoci zasu tsunduma yajin aiki ranar Litinin Source: Twitter
Asali: Twitter

Uyilawa ya kara da cewa,

"Kuna da labari mun rasa 19 daga cikin mambonimu a sanadiyyar Korona kuma ya kamata a biya insorar mutuwa kan aiki ga magajinsu.
"Wancan karen da muka ziyarci ministan ayyuka da na lafiya, ance mana mambobinmu suna cikin wadanda zasu ci gajiyar inshorar amma sai muka tarar da sunayensu baya wurin.

Ya kara da yadda gwamnatin tarayya ta gaza cimma bukatun likitoci, wannan yana daga cikin abinda yasa suka yanke hukuncin shiga yajin aikin

Har ila yau, Shugaban hukumar yana baiwa yan Nijeria hakuri akan wannan hukuncin yana mai cewa gazawar gwamnati wurin sauke hakkinta ne ya janyo haka.

Abinda aka cimma a karshen taron

Bayan dukkan nazari akan rawar da gwamnatin tarayya dana jiha suka taka akan abinda ya shafi cigaban mambobinmu da kuma gazawar gwamnati wurin biyan bukatun mu bayan kwanaki dari da sha uku, majalisar zartarwa ta yanke hukuncin shiga yajin aikin sai baba ta gani daga karfe 8 na ranar Litinin 2 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Kwararrun likitocin Najeriya za su tsunduma yajin aiki

Buratai fa so yayi a mika masa Igboho, amma gwamnatin kasar Benin taki: Femi Falana

A wani labarin, Shahrarren Lauya, Femi Falana, ya bayyana yadda gwamnatin jamhuriyyar Benin ta watsawa Ambasadan Najeriya dake kasar, Tukur Buratai, kasa a ido.

Falana yace hakan ya faru ne lokacin da hukumomin kasar suka bayyanawa Buratai cewa zasu bi doka ne wajen mayar da Sunday Igboho Najeriya.

Igboho wanda ke daure a kurkukun jamhurriyar Benin yanzu ya shiga hannun hukumar Kotono ne ranar 19 ga Yuli yayinda yake kokarin guduwa kasar Jamus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel