‘Ya ‘yan Nasiru Kabara 18 sun rubutawa Shugaban kasa takarda, sun wanke Sheikh Abduljabbar

‘Ya ‘yan Nasiru Kabara 18 sun rubutawa Shugaban kasa takarda, sun wanke Sheikh Abduljabbar

  • Wasu daga cikin ‘Ya ‘yan Nasiru Kabara 18 sun kai wa Shugaban kasa kukansu
  • ‘Yan gidan Nasiru Kabara sun rubuta takarda, suna wanke Abduljabbar Kabara
  • Wadannan Bayin Allah sun zargi Malaman Kano da yi wa ‘danuwan na su sharri

Kano - ‘Ya ‘ya 18 daga gidan darikar Qadiriyya watau Sheikh Nasiru Kabara, sun rubuta takarda ta musamman zuwa ga fadar shugaban kasar Najeriya.

Wadannan mutane sun bukaci gwamnatin tarayya ta tsoma bakin ta a cikin abin da ta ka kira muzguna wa ‘danuwanta, Abduljabbar Nasiru Kabara.

Jaridar Daily Nigerian ta samu labarin wannan wasika da ta fito daga gidan na Qadiriyya a jihar Kano.

A wannan takarda, ‘yanuwan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sun wanke shehin daga zargin da ake yi masa, suka ce an jirkita karatun da ya gabatar.

Wadannan shehunnai; maza da mata sun shaida wa shugaban kasa cewa an bankara karatun Abduljabbar Kabara ne domin a kama shi da laifin batanci.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Hadiman Sunday Igboho, Ta Fadi Dalili

Abin da wasikar ta kunsa

“Tare da girmama wa da kan-kan da kai gare ka ran ka ya dade, mu ‘ya ‘ya (maza da mata) na Maulana Sheikh (Dr.) Muhammad Nasiru Kabara, mu na bukatar mu kawo kuka a gabanka, a matsayinka na shugaba kuma uban kowa, wanda ba zai taba goyon bayan rashin adalci ba.”
“Muna amfani da wannan dama domin kawo korafi game da ‘danuwan mu na jini, Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara, wanda wasu malaman Kano suka taso a gaba saboda sabani na gaira babu dalili, da yake tsakaninsu.”
“Wannan sabani ya jawo suka rika murguda karatuttukan ‘danuwanmu da aka dauka, domin su yi masa sharrin cin zarafin Annabi Muhammad (SAW), da nufin a kassara shi gaba daya.”
"Muna tabbatar maka cewa duk zargin da wadannan ‘malamai’ suke yi a kan ‘danuwanmu, kage ne, da gangan aka kirkiro su saboda manufa."

Sheikh Abduljabbar
Sheikh Abduljabbar Kabara Hoto: BBC / Aliyu Samba
Asali: UGC

Shehunan suka ce abin da ake kokarin laka wa ‘danuwansu, shi ne abin da yake ta yaki da shi.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

Wadanda suka sa hannu a takardar

Daily Nigerian ta kawo sunayensu kamar haka, daga ciki akwai maza biyar, da kuma mata 13.

1. Sheikh Ibrahim Mu’azzam Sheikh Nasir Kabara

2. Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Sheikh Nasir Kabara

3. Malam Askiya Sheikh Nasir Kabara

4. Malam Yahya Sheikh Nasir Kabara

5. Malam Aburumana Sheikh Nasir Kabara

6. Sayyidah Saratu Sheikh Nasir Kabara

7. Sayyidah Nafisatu Sheikh Nasir Kabara

8. Sayyidah Khudriyyah Sheikh Nasir Kabara

9. Sayyidah Zam’atu Sheikh Nasir Kabara

10. Sayyidah Saffanatu Sheikh Nasir Kabara

11. Sayyidah Aishatu Mannubiyyah Sheikh Nasir Kabara

12. Sayyidah Ummu Aimanal Habashiyyah Sheikh Nasir Kabara (I)

13. Sayyidah Khadijatul Habashiyyah Sheikh Nasir Kabara (II)

14. Sayyidah Huza’iyyah Sheikh Nasir Kabara

15. Sayyidah Jamila Sheikh Nasir Kabara

16. Sayyidah Bulkisu Sheikh Nasir Kabara

17. Sayyidah Rukayya Sheikh Nasir Kabara

18. Sayyidah Hansa’u Sheikh Nasir Kabara

‘Yanuwan malamin sun kira kansu da UNITED FORUM OF SHEIKH NASIR KABARA’S DESCENDANTS, ma’ana kungiyar hadin-kan tatson Nasiru Kabara.

Jagoran gidan a nan shi ne Sheikh Sidi Musal Qasiyuni Nasiru Kabara. Legit.ng Hausa ta lura babu hannun Sheikh Qaribullahi Kabara a wannan budaddiyar wasika.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sheikh AbdulJabbar Kabara ya gurfana gaban kotun Shari'a

Hukuma ta tsare Abduljabbar Nasiru Kabara a kurkuku

Kwanaki hukuma ta tsare Abduljabbar Nasiru Kabara a kurkuku bisa umarnin Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje bayan malaman Kano sun yi fito-na-fito da shi.

Bayan an yi mukabala tsakanin bduljabbar Kabara da sauran malamai, wasu Mabiya Abduljabbar Kabara sun fara fitowa, su na tuba, suka ce sun fahimci gaskiya a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel