Duka Ma’aikatan fadar Shugaban kasa sun dauki rantsuwar hana sirri fita daga Aso Rock

Duka Ma’aikatan fadar Shugaban kasa sun dauki rantsuwar hana sirri fita daga Aso Rock

  • Ma’aikatan fadar Aso Rock sun dauki rantsuwa cewa za su tsare sirrin Gwamnati
  • An kawo wani Alkali ya lakkana wa Ma’aikatan rantsuwa a fadar Shugaban kasa
  • Gwamnati za ta dauki mataki a kan wanda aka samu ya karya rantsuwar da ya yi

Abuja - Rahotanni daga The Cable sun tabbatar da cewa an gargadi ma’aikatan da ke fadar shugaban kasa a kan fitar da bayanan sirri zuwa waje.

Sakataren din-din-din ya yi wa jami'ai kashedi

An ja-kunnen ma’aikatan ne bayan sun yi wata rantsuwar rike sirrin fadar shugaban Najeriyar.

Sakataren din-din-din na fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya yi wa ma’aikatan wannan kashedi a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, 2021, a birnin Abuja.

Tijjani Umar ya bayyana wa ma’aikatan cewa sakin baki da tozarta bayanan sirrin fadar shugaban kasa babban laifi ne da za su jawo a hukunta mutum.

“Ina so in fara jawabi da cewa wannan aiki da aka yi shi ne zai sa mu fara yin abin da ya dace a ofisoshinmu.”

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gidan ya cabe, bangaren Lai Mohammed sun sa sharadin barin APC

“Fitar da bayanai da takardun sirri ya na kawo tasgaro wajen aiki. Saboda haka ne mu ka ga bukatar taimaka wa masu yada bayanan da suke na sirri.”
Aso Rock
Ana taro a fadar Aso Villa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

“Nan ba wuri ne kasafai ba, don haka yake da muhimmanci a tunatar da ku nauyin da ke kanku, rantsuwar da kuka yi da hukuncin da ke tattare da saba doka.”
“Gwamnati ta na aiki ne da jerin wasu dokoki da sharuda, kuma dole ne a girmama wadannan dokoki da sharudodi, kuma saba masu yana tare da hukunci.”

Rantsuwa za ta ji har ma'aikatan da su ka ajiye aiki

Jaridar Premium Times ta ce Alkalin wani babban kotu da ke birnin tarayya Abuja, Hamza Muazu ya lakkana wa ma’aikatan wannan rantsuwa a Aso Villa.

Umar ya ce doka za ta yi aiki kan duk wanda ya saki bakinsa, ya na baza bayanan da ba su dace a ji su a fili ba, ko da kuwa ma’aikacin ya yi ritaya daga aiki.

Kara karanta wannan

Cikin mako guda: 'Yan bindiga sun kashe mutum 48, da kona sama da gidaje 300 a Kaduna

Kwanakin baya ne aka ji cewa barayi sun yi yunkurin fada wa cikin gidan shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari a Aso Rock.

Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya shaida wa Duniya hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel