APC za ta kori wasu jiga-jiganta bayan an samu rigingimu da rabuwar kai a zabukan Jam’iyya

APC za ta kori wasu jiga-jiganta bayan an samu rigingimu da rabuwar kai a zabukan Jam’iyya

  • Rigimar cikin gidan Jam’iyyar APC ya fito fili a wajen zabukan da aka shirya
  • APC ta gagara samun hadin-kan ‘ya ‘yanta a Ogun, Oyo, Ekiti, Kwara, Ebonyi
  • Akwai jihohin da aka rika harbe-harben bindiga, har hakan ya sa aka rasa rai

Najeriya- Rahotoa daga The Cable ya nuna jam’iyyar APC ta gamu da rikici iri-iri a yunkurin da ta ke yi na zaben shugabannin mazabun da ke kananan hukumomi.

An kashe mutum wajen harbe-harbe a Ekiti

Jaridar ta ce rikicin da aka yi a Ekiti ya yi sanadiyyar kashe wani tsagera a wata mazaba da ke karamar hukumar Ado Ekiti, kuma an ta jin karin harbin bindiga.

Shugaban kungiyar SWAGA, Tony Adeniyi ya ce babu zaben da aka gudanar a fadin jihar Ekiti.

An yi arangama a jihar Ogun

A jihar Ogun, sabanin da ke tsakanin yaran gwamna Dapo Abiodun da Sanata Ibikunle Amosunya sun jawo an fitar da shugabanni dabam-dabam a zabukan da aka yi.

Kara karanta wannan

Bayan APC ta sha da kyar a kotu a zaben Gwamna, Minista ya ce za a iya rasa zaben 2023

Rahoton da aka samu ya tabbatar da cewa an ji wa wani mutum daya ciwo a wajen wannan zabe.

Hakan ta faru a zabukan Oyo

Sabanin Ministan wasanni, Sunday Dare da na tsohon gwamna Adebayo Alao-Akala ya fito fili a jihar Oyo, an gaza shawo kan wannan rikici a yankin Ogbomoso.

Taron APC
Gangamin APC a Ogun Hoto: www.icirnigeria.org
Asali: UGC

Rikici ya barke a Ebonyi, Akwa Ibom da Bayelsa

An samu labarin harbe-harbe a wata makaranta da ke Ugwuachara a Ebonyi. Ana zargin wani ‘dan siyasa da tura 'yan bindiga su tarwatsa zaben da aka shirya.

A Akwa Ibom wasu matasa sun kona sakatariyar APC, suna zargin John Akpanudoedehe da katsalandan, suka ce ya na neman ya kakaba masu ‘yan takara.

Bangarori sun ja daga Bayelsa

Masu goyon bayan Ministan Neja-Delta, Timipre Sylva da magoya baya tsohon Minista, Heineken Lokpobiri, sun bi umarnin kotu, amma har yanzu ba a ga maciji.

Punch ta ce shugabannin rikon kwarya na APC a karkashin Mai Mala Buni sun ce ba za su yarda da abin da ‘yan taware suke yi ba, za a hukunta duk masu laifi.

Kara karanta wannan

Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo

A baya an ji cewa ana rade-radin babban Jigon APC a yankin kudu maso yamma, Asiwaju Bola Tinubu ya na kwance a asibitin kasar waje, har an yi masa aiki.

Mai magana da yawun bakin Bola Tinubu ya ce mai gidansa yana nan lau, babu abin da ya faru da shi, yace dama an saba yi masa sharrin ya mutu tun ba yau ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel