Bayan APC ta sha da kyar a kotu a zaben Gwamna, Minista ya ce za a iya rasa zaben 2023

Bayan APC ta sha da kyar a kotu a zaben Gwamna, Minista ya ce za a iya rasa zaben 2023

  • Festus Keyamo ya rubuta wa shugabannin jam’iyyar APC wata takarda a boye
  • Ministan ya ba APC shawarar dakatar da maganar shirya zaben shugabanninta
  • Keyamo ya ce hukuncin kotun koli ya nuna bai dace Mala Buni ya rike APC ba

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo, ya yi sharhi a kan abin da ya faru a kotun koli a shari’ar zaben gwamnan jihar Ondo.

Karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasan ya yi kira ga jam’iyyar APC ta janye maganar gudanar da zaben shugabannin da ake shirin yi.

Kamar yadda Premium Times ta kawo rahoto a ranar Laraba, Keyamo, ya kawo wannan magana ne bayan hukuncin da kotun koli ta yi kan zaben Ondo.

Wasu daga cikin Alkalan babban kotun na Najeriya sun yanke hukunci cewa nada gwamna Mai Mala Buni a matsayin shugaban APC ya ci karo da doka.

Kara karanta wannan

Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo

Ministan ya fitar da wata takarda a boye zuwa ga shugabannin jam’iyya, ya ce rikici zai iya barke wa a APC muddin aka gudanar da zabukan shugabanni.

Ondo 2020: Jam’iyyar APC ta sha da kyar a kotun koli

Festus Keyamo wanda babban lauya ne, ya shaida wa APC cewa saura kiris da ‘dan takarar PDP a zaben Ondo, Eyitayo Jegede ya yi masu illa a kotun koli.

Keyamo ya na ganin nan gaba ba dole ba ne jam’iyyar APC ta taki sa’ar da ta samu yanzu. Idan aka samu bacin rana, APC za ta iya samun kanta a matsala.

Bayan APC ta sha da kyar a kotu a zaben Gwamna, Minista ya ce za a iya rasa zaben 2023
Mala Buni da Shugaban kasa Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

“Abin da ya ceci gwamna AKEREDOLU shi ne Jegede bai cusa Gwamna Mai Mala Buni a shari’ar ba. Jegede ya na kalubalantar gwamna ya rike jam’iyya.”

A cewasa, nada gwamna a matsayin shugaban rikon kwaryan jam’iyya, ya saba sashe na 17 na dokar APC, don haka ya ce a bar wa BOT dawainiyar zabe.

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya caccaki mulkin APC, ya ce za ta ruguza Najeriya kafin 2023

Jaridar The Nation ta rahoto Keyamo ya na cewa kotu za ta iya nakasa APC tun daga farko har karshenta idan har aka yi wasa da hukuncin da kotun koli ta yi.

Jam'iyyar PDP za ta shiga cikin fagamniya

Amma sai dai kuma hadimin shugaban kasa, Femi Adesina ya ganin cewa jam'iyyar PDP za ta daidaice, ta gigice, ‘ya ‘yan ta su yi ta sauya-sheka kafin 2023.

Hakan na zuwa ne bayan PDP ta ce Muhammadu Buhari ya maida Aso Villa wurin taron APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel