Ana rade-radin Tinubu ya na kwance a asibitin kasar waje, Hadiminsa ya fito ya yi magana

Ana rade-radin Tinubu ya na kwance a asibitin kasar waje, Hadiminsa ya fito ya yi magana

  • Ana ta yawo da jita-jita cewa Asiwaju Bola Tinubu ya na kwance a kasar waje
  • Mai magana da yawun bakin ‘dan siyasar ya yi jawabi, ya karyata rade-radin
  • Tunde Rahman ya ce ba jinyar rashin lafiya ta kai Bola Tinubu kasar wajen ba

Legas - Rahotanni daga Sahara Reporters suna yawo cewa an kwantar da tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, a wani asibiti a kasar waje.

Mai ba magana da yawun bakin babban ‘dan siyasar, Tunde Rahman, ya yi jawabi a ranar Asabar, 31 ga watan Yuli, 2021, inda ya karyata wannan rade-radi.

Tunde Rahman ya yi magana da jaridar Punch dazu, inda ya tabbatar da cewa mai gidansa ya na kasar waje a halin yanzu, amma ya ce ba jinya yake yi ba.

Kamar yadda Tunde Rahman ya yi bayani, babu abin da yake damun Asiwaju Bola Tinubu a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka cafke wani da ake zargin yana karbar kudin fansa ta asusun banki

“Mai girma Asiwaju Bola Tinubu ya nan lafiya. Ya na nan kalau kuma garau. Ba ya asibiti, bai fama da wata rashin lafiyar da za ta jawo a kwantar da shi.”
“Eh ba ya kasar nan a halin yanzu. Zai dawo ba da dade wa ba.”

Muhammadu Buhari da Bola Tinubu
Muhammadu Buhari da Bola Tinubu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“Duk lokacin da ya bar kasar nan, abin da za a fara ji shi ne wasu miyagun mutane suna yada labari cewa bai da lafiya, ya na kwance a asibiti, ko ya mutu.”
“Abin takaici ne masu yada wannan sharrin ba su gajiya da wannan aiki, a duk lokacin da suka fara yada labarin bogi, sai ya (Tinubu) fito, ya kunyata su.”
“Su wanene ke tsoron Asiwaju Tinubu? Masu yi wa Tinubu sharri ko fatan ya mutu, su bi a hankali, su sani rai da mutuwa duk suna hannun Ubangiji ne.”

Sannan Vanguard ta kawo jawabin da yamman nan, kamar yadda shafin Bola Tinubu Ambassadors na magoya bayan Tinubu suka wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan Najeriya za su iya amfani da zaben 2023 don gyara kuskuren da suka yi, Bishop Kukah

Mutuwar Tinubu: Ba yau farau ba

Kwanakin baya an yi ta rahoto cewa kafafen sada zumunta sun cika da jita-jitar cewa Bola Tinubu ya mutu, amma hadiminsa sun karyata rahotannin karyan.

Bayan makonni biyu da yada wannan labari na bogi, sai aka koma cewa an yi wa tsohon gwamnan na jihar Legas aiki a wani asibiti da ke Maryland, Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel