Abin da ya sa Gwamnatin Kaduna ta sake maida Sheikh Zakzaky da matarsa kotu inji Falana

Abin da ya sa Gwamnatin Kaduna ta sake maida Sheikh Zakzaky da matarsa kotu inji Falana

  • Femi Falana ya yi magana game da shari’ar Gwamnati da Ibrahim Zakzaky
  • Babban Lauyan ya yi tir da daukaka karar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi
  • A wani jawabi da Falana ya fitar, ya jinjina hukuncin da kotun tarayyan ya yi

Abuja - Babban lauyan nan da ya yi suna wajen kare hakkin Bayin Allah a Najeriya, Femi Falana ya yi tir da yunkurin da gwamnatin jihar Kaduna ta ke yi.

Gwamnatin Kaduna ta sake kai karar shugaban kungiyar IMN, Ibrahim El-Zakzaky gaban kotu, jim kadan bayan malamin da mai dakinsa sun samu ‘yanci.

Femi Falana wanda ya jagoranci lauyoyin da suka kare Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa, Zeenat El-Zakzaky, ya soki matakin da gwamnati ta dauka.

Channels TV ta fitar da rahoto, inda aka ji Femi Falana SAN ya na cewa gwamnatin Kaduna ta dage ido rufe ne a kan sai ta kassara wadanda ake tuhumar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

Shugaban lauyoyin da suka tsaya wa malamin da mai dakinsa yake cewa gwamnatin Kaduna ta na so ta cigaba da tsare Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da iyalinsa.

Falana ya fitar da jawabi, ya yi Allah-wadai da gwamnati

“Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da sabon karar ne bayan an fahimci cewa za mu yi nasara a hukuncin da aka zartar a ranar 28 ga watan Yuli.”
“Mai shari’a ya yi fatali da korafi takwas da aka gabatar saboda an shigar da karar abin da aka yi a 2015, ana so ayi hukunci da dokar da aka kawo a 2017.”

Sheikh Zakzaky
Shugaban kungiyar IMN, Ibrahim El-Zakzaky Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Kotu ta saurari shaidu 15 da gwamnati ta kawo, ta ce wanda ake zargi bai aikata laifi ba, ta wanke shi.”

Femi Falana ya jinjina wa hukuncin da aka yi

The Cable ta ce lauyan ya yabi Alkalin da ya zartar da wannan hukunci ba tare da nuna wani tsoro ba.

Kara karanta wannan

Awannni da samun ‘yanci, Gwamnati za ta sake maka Ibrahim Zakzaky a kotu kan sabon zargi

Falana ya ce Alkalin da ya saurari wannan shari’a ya nuna jajirce wa da gwarzantan da ba a saba gani ba, tare da yin abin da ya kamata duk da barazanar wasu gungu.

Ba mu gamsu ba - Gwamnati

A baya an ji cewa gwamnati ta sake kai karar malamin shi'an gaban kotu ne kusan sa’o’i 24 bayan Alkali ya wanke shi da mai dakinsa daga duk zargin da ke kansu.

Gwamnatin Nasir El-Rufai ba ta gamsu da hukuncin da Alkali Gideon Kurada ya yi ba. Lauyan gwamnati, Esq. Dari Bayero, ya ce gaskiya ba ta yi a shari'ar aiki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel