Awannni da samun ‘yanci, Gwamnati za ta sake maka Ibrahim Zakzaky a kotu kan sabon zargi

Awannni da samun ‘yanci, Gwamnati za ta sake maka Ibrahim Zakzaky a kotu kan sabon zargi

  • Gwamnatin Kaduna ba ta gamsu da shari’ar kotun tarayya a kan Ibrahim Zakzaky ba
  • Lauyan da ya tsaya wa Gwamnati a kotu ya ce hukuncin da aka yi ya saba wa gaskiya
  • Su kuma Lauyoyin Ibrahim Zakzaky suna cewa za su nemi diyya a hannun Gwamnati

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta kuma shigar da wasu kara a kan shugaban kungiyar IMN, Ibrahim El-Zakzaky da ya yi shekaru ya na hannun hukuma.

Daily Trust ta ce gwamnati ta sake kai karar malamin gaban kotu ne kusan sa’o’i 24 bayan Alkali ya wanke shi da mai dakinsa daga duk wasu zargi da ke kansu.

Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ba ta gamsu da hukuncin da Alkali Gideon Kurada ya zartar a ranar Laraba, 28 ga watan Yuli, 2021, su ke shirin sake kai kara.

Babban lauyan da ya tsaya wa gwamnati a shari’ar, Esq. Dari Bayero, ya shaida wa Jaridar cewa babu shakka gwamnatin Kaduna za ta dauka kara zuwa gaba.

Kara karanta wannan

El-Zakzaky: Lauyoyin Shehin Shi'a za su nemi diyya daga wajen Gwamnatin El-Rufai a Kotu

“Za mu daukaka kara, babu shakka kan wannan. Har ma mun samu takardar hukuncin kotun domin sam ba mu yarda da hukuncin mai girma, mai shari’a ba.”

Lauyan yake cewa hukuncin da Alkali ya yanke, ya ci karo da gaskiyar da aka gabatar masa a kotu.

Ibrahim Zakzaky
Sheikh-Ibrahim Zakzaky Hoto: www.iqna.ir

Me lauyoyin Zakzaky suke shirin yi?

Bayan samun nasara a kotun tarayyan, an ji lauyoyin shugaban kungiyar IMN, su na bayanin cewa za su koma kotu domin su nemi gwamnati ta biyya su diyya.

Zakzaky da iyalinsa za su kalubalanci Gwamnati kan tsare su da aka yi tun 2015 tare da muzgunu wa, wani lauya ya ce sai an biya su alhakin wannan cin zarafi.

Ina Zakzaky ya shiga bayan ya samun ‘yanci

A daidai wannan lokaci kuwa shugaban na kungiyar mabiya shi’an, Ibrahim El-Zakzaky da mai dakinsa, Zeenat El-Zakzaky, sun bar Kaduna, sun wuce Abuja.

El-Zakzaky ya wuce birnin Abuja ta jirgin sama, inda likitoci za su duba shi. Malamin ya yi kokarin zuwa Abuja tun a ranar Laraba, amma sai a jiya ya tafi.

Kara karanta wannan

Saura awanni 48 ayi zabe, an taso Mai Mala Buni da 'yan kwamitinsa su ajiye shugabancin APC

Rahotanni sun ce malamin ya kwana a Kaduna tare da iyalinsa ranar Laraba, sai ya wuce Abuja jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel