Mayaƙan Boko Haram Da Iyalansu Su 91 Sun Miƙa Wuya a Borno, Rundunar Sojojin Nigeria

Mayaƙan Boko Haram Da Iyalansu Su 91 Sun Miƙa Wuya a Borno, Rundunar Sojojin Nigeria

  • Rundunar sojojin Nigeria ta ce yan Boko Haram/ISWAP su 91 sun mika wuya a Borno
  • Kakakin Rundunar Sojoji Onyema Nwachukwu ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a a Abuja
  • Nwachukwu ya kuma ce dakarun sojojin da yan sa-kai sunyi nasarar kama dan sakon yan ta'adda

FCT, Abuja - Rundunar sojojin Nigeria ta ce da ke dakarunta na Operation Hadin Kai (OPHK) sun karbi wasu mayakan kungiyar Boko Haram da ISWAP su 91 da iyalansu da suka mika wuya a baya-bayan nan, The Cable ta ruwaito.

A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojojin Nigeria ya sanar da hakan a ranar Juma'a a Abuja.

Nwachukwu ya ce yan ta'addan sun mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai da ke aikin sintiri na kakabo sauran yan ta'addan da suka yi saura a yankin.

Yan Boko Haram Da Iyalansu Su 91 Sun Miƙa Wuya a Borno, Rundunar Sojojin Nigeria
Mayaƙan Boko Haram Da Iyalansu Su 91 Sun Miƙa Wuya a Borno, Rundunar Sojojin Nigeria. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Da duminsa: IG yan sanda ya bada umurnin kaddamar da bincike kan zargin da ake yiwa Abba Kyari

Ya ce dakarun Bataliya ta 202 sun karbi yan ta'adda takwas da iyalansu da suka hada da manya mata 10 da yara 22, da suka mika wuya a kauyen Ruwaza da ke karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

Daily Trust ta ruwairo cewa Nwachukwu ya kuma ce dakarun Forward Operational Base (FOB) da ke aiki a hanyar BoCobs zuwa Bama sun kama yan ta'adda 20 da iyalansu da suka mika wuya go sojojin a kauyen Nbewa da ke karamar hukumar Bama.

A cewarsa, akwai mata manya 15 da yara 15 cikin iyalan da suka mika wuya.

Ya ce:

"Dukkan wadanda ake zargin su mika kai ga dakarun yayin sintiri da suka yi a yankin a ranar 29 ga watan Yuli, bayan tsananta sintiri da sojojin ke yi a yankin a halin yanzu."
"An yi wa yara daga cikin wadanda suka mika wuyan rigakafin cutar shan inna, yayin da manya maza da mata suna nan ana musu tambayoyi bayan an musu tantancewa na farko."

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke 'yan bindiga 14, an damke masu kai musu bayanai 16, dabbobin sata 223

Sojojin sun kama dan sakon Boko Haram, sun kwato kayayyaki

Har wa yau, kakakin sojojin ya ce sojojin 73 Battalion tare da hadin gwiwa da yan sa-kai na JTF da mafarauta sun kama wani mai siyo wa yan ta'adda kayayakin ayyuka yayin sintiri a hanyar Molai zuwa Damboa.

Ya ce cikin gaggawa tawagar jami'an tsaron suka shiga wurin suka kama wanda ake zargin yayin da ya ke kintsawa ya tafi kai wa yan ta'adda kayayyaki a daji.

Nwachukwu ya ce kayayyakin da aka kwato hannun wanda ake zargin sun hada da motan hawa daya, jarkoki hudu na man fetur (lita 30), galan daya na injin oyel (lita 4), man juye na inji, tocila, da na'urar saka wa tayan babur iska.

Sauran kayan sun hada da gidan sauro, dadumar salla biyu, bargo biyu, spana 2, batiri pakiti 10, da gam guda 36.

Sai kuma kyandir pakiti biyar, pakitin dunkulen dandano biyar da wasu hatsi da ya auno

Kara karanta wannan

Matasan NYSC 5 sun rasa rayukan sakamakon mumunan hadari a Abuja

Dogo Nabajallah: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan Katsina Ya Gamu Da Ajalinsa Sakamakon Rikicin Neman Aure

A wani labarin daban, rikici ya barke tsakanin bangarorin ƴan bindiga biyu masu adawa da juna a Katsina wadda ya yi sanadin mutuwar shugaban yan bindiga, Nabajallah, da wasu yan bindigan uku, rahoton The Punch.

Majiyoyi sun ce an kashe shugaban yan bindiga, Dogo Nabajallah a cikin dajin Dungun Muazu da ke karamar hukumar Sabuwa a ranar Laraba.

A cewar rahoton Premium Times Hausa wasu ƴan bindigan da ke adawa da shi ne suka afka masa suka kashe shi saboda rikicin neman aure da ke tsakanin yaronsa da bangaren su yan adawan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel