Najeriya Ba Zata Koma Ruwa Ba, APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Atiku

Najeriya Ba Zata Koma Ruwa Ba, APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Atiku

  • Jam'iyyar APC mai mulkin kasar nan tace sam Najeriya ba zata koma ruwa ba
  • APC ta faɗi hakane ta bakin sakatarenta, John Akpanudoedehe, ranar Jumu'a domin martani ga Atiku
  • Atiku ya yi ikirarin cewa yan Najeriya Allah-Allah suke PDP ta dawo mulki a 2023

FCT Abuja:- Jam'iyyar APC tace Najeriya ba zata koma ruwa ba ƙarkashin mulkin PDP a shekarun baya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

APC ta faɗi hakane domin maida martani kan maganar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.

APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Atiku
Najeriya Ba Zata Koma Ruwa Ba, APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Atiku Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wace magana Atiku Abubakar ya yi?

A ranar Alhamis, bayan ganawa da Gwamna Wike na jihar Rivers, Atiku yace yan Najeriya Allah-Allah suke PDP ta dawo kan mulki a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, yace:

"Na yi imani cewa yan Najeriya sun kosa 2023 ta zo saboda jam'iyyar PDP ta dawo kan madafun iko."
"Na shekara sama da 70 a duniya amma ban taɓa ganin Najeriya ta lalace kamar yadda take yanzun ba, ta ɓangaren kalubalen tsaro, rashin aikin yi, ban taba gani ba domin abun yayi muni sosai."

Kara karanta wannan

Gwamna Buni Ya Yi Watsi da Hukuncin Kotun Koli, Ya Na Nan Daram a Shugaban APC

APC ta maida zazzafan martani

Amma da yake martani kan maganar Atiku, Sakataren kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, John Akpanudoedehe, yace Najeriya ba zata koma ruwa ba.

Dailytrust ta ruwaito sakataren APC yana cewa:

"Ya kamata Atiku yasan cewa yan Najeriya ba zasu koma kasar Masar ba, ba zasu sake komawa ruwa su zaɓi PDP ba a 2023 bayan sun gwada sunga gazawarta."
"Ta wani fannin ma zance babu wani abu mai kyau dake fitowa daga PDP, sun rike Najeriya na tsawon shekara 16 amma babu wata nasara da zasu iya nuna wa."
"Nasarorin da jam'iyyar mu ta APC ta samu a ƙasa da shekara 8 sun shafe mulkin da PDP ta yi na shekara 16. APC ba tsarar PDP bace ta kowane fanni."

A wani labarin kuma Babu Wanda Zai Ci Nasara Fiye da Matakin Karatunsa, Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa babu wanda zai ci nasara fiye da ilimin da yake da shi

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Najeriya Sama da Miliyan 60m Sun Mallaki Lambar NIN, NIMC

Buhari ya faɗi haka ne a wurin taro kan Ilimi na duniya dake gudana a birnin Landan na kasar Burtaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags:
APC