Muna Mika godiya ga Yan Nijerian da suka tsaya mana lokacin shari'ar mu, Iyalan Zakzaky

Muna Mika godiya ga Yan Nijerian da suka tsaya mana lokacin shari'ar mu, Iyalan Zakzaky

  • Iyalan gidan Zakzaky sun mika godiyarsu ga yan Nijeria da suka tsaya musu har karshen shari'arsu
  • Wannan na kunshe a jawabin da dan Zakzaky ya saki ranar Alhamis
  • A karshe ya kuma mika godiyarsa ga bajintar Iyayensa

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Iyalan gidan Zakzaky sun mika godiyarsu ga yan Nigeria da suka tsaya musu a lokacin shari'ar su wacce ta dauki tsawan kwana dubu biyu da hamsin da biyar wanda yayi daidai da kusan shekaru 6.

A wani jawabi da dan Ibrahim Zakzaky, Mohammad El-Zakzaky ya saki ranar Alhamis a madadin iyalan gidan, ya nuna godiya ga Allah da farin cikinsu matuka ga wadanda suka tsaya musu yayin shariarsu wacce ta dauki tsawon shekara shida.

Muna Mika godiya ga Yan Nijerian da suka tsaya mana lokacin shari'ar mu, Iyalan Zakzaky
Muna Mika godiya ga Yan Nijerian da suka tsaya mana lokacin shari'ar mu, Iyalan Zakzaky
Asali: Facebook

Abinda jawabin ya kunsa

Jawabin yace:

"Kamar yadda kuka sani jiya(Laraba) an saki Mahaifina Sheikh Ibrahim Zakzaky da Mahaifiyata Zeenah Ibrahim bayan kotu ta wanke su daga zargin da gwamnatin Kaduna ta ke musu.

Kara karanta wannan

Hotunan Sheikh Ibrahim Zakzaky Ba Tare da Jami'an Tsaro ba Karon Farko Cikin Shekaru 6

Bayan godiya ga Allah madaukakin Sarki muna godiya ga wadanda suka tsaya mana yayin shariarmu wacce ta dauki tsawon shekara shida.
"Ni da daukacin iyalina muna godiya matuka ga maza, mata da yara da suka tsaya tsayin daka akan rashin adalci, suka bayar da ransu wajen tabbatar da cewa anyi adalci a garesu(mahaifana) a ciki da wajen kasar nan.
Muna godiya kuma matuka da jaruman da suka yi ta sintiri Abuja a kullum har tsawon shekara biyar, wannan shine babban sadaukarwa wadda ba'a cika samu ba a tarihin Nigeria.
Ina kuma mika godiyata ga kungiyar kare hakkin bil'adama wacce ta cigaba da taimaka mana da muryoyinsu a yanayin nan mai wahala, musamman kungiyar kare hakkin bil'adama, kungiyar kare hakkin bil'adama a musulunci da suka tabbatar da cewa ba'ayi rufa rufa a abinda ya auku a shekarar 2015.
'Muna mika jinjinarmu ga kafofin watsa labarai da yan jarida wadanda suka dage akan gaskiya duk da fuskantar kulubale, barazana da kuma tarzoma.

Kara karanta wannan

El-Zakzaky: Lauyoyin Shehin Shi'a za su nemi diyya daga wajen Gwamnatin El-Rufai a Kotu

'Muna godiya kan bajintar ku da dagewarku duk tsawon lokacin da kuka ki juya idanunku wajen ta'addanci da wasu laifuka da ake aikatawa da sunan jihar.
"A karshe ina mika godiyata ga bajintar iyayena da kuma adilan mashar'anta a karkashin jagorancin Babban lauya cif Femi Falana, wanda duk yadda aka kai ga ja da jinkirta shari'ar amma suka tsaya tsayin daka akai, muna matukar godiya da kokarinku."

Kotu ta dakatar da shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara

A gefe guda, wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da umarnin hana majalisar dokokin jihar Zamfara tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kotun ta bayar da wannan umarni ne a ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, bayan duba karar da Ogwu James Onoja ya shigar a madadin jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng