Gwamna Ya Gano Ma'aikatan Bogi 7,161 a Jiharsa, Ya Zare Su Daga Tsarin Albashi
- Gwamnatin jihar Bauchi ta gano wasu ma'aikata 7,161 da aka kutsa cikin tsarin biyan albashi ba bisa ka'ida ba
- A wani bincike da mataimakin gwamna ya jagoranta, Gwamnatin ta ɗauki matakin zaresu daga tsarin baki ɗaya
- Gwamna Bala Muhammed, ya nuna matukar jin dadinsa tare da mika godiya ga kwamitin bincike
Bauchi:- Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa ta gano ma'aikatan bogi 7,161 kuma ta cire su daga tsarin biyan albashi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Ma'aikatan bogin sun kunshi waɗanda ke aiki da gwamnatin jiha da kuma na ƙananan hukumomi da kuma yan fansho.
Gwamnatin ta gano su ne bayan gudanar da bincike a shafin yanar gizo na ma'aikatan jihar baki ɗaya.
Kwamitin binciken bisa jagorancin mataimakin gwamna, Sanata Baba Tela, sun mika rahoton kwamitinsu ga gwamna Bala Muhammed jiya a Bauchi.
Me rahoton kwamitin ya kunsa?
Tela ya bayyana cewa kimanin naira miliyan N511m aka ceto duk wata bayan sallamar waɗannan ma'aikatan daga jerin masu karbar albashi.
Mataimakin gwamnan, Yace:
"Kwamitin mu ya gano cewa ma'aikata 80,236 aka ɗora a shafin yanar gizo na ma'aikatan Bauchi wanda suka haɗa da na jiha da kananan hukumomi."
"Ma'aikata 29,752 ne a karkashin gwamnatin jiha yayin da akwai 50,484 a kananan hukumomin dake faɗin jiha."
"Muna bada shawarar a ɗauki matakin ladabtarwa ga waɗanda suka karya dokar sabon tsarin biyan albashi da suka haɗa da manajojin kula da tsarin dake jiha da na kananan hukumomi."
Tela ya kara da cewa ya kamata a naɗa kwamiti na musamman da zai rinka sa ido kan yadda lamarin ke tafiya kuma ya dinga kawo rahoto akai-akai ga bangaren zartarwa.
Gwamna Ya nuna jin dadinsa
Da yake martani, Gwamna Bala Muhammed, ya gode wa kwamitin bisa wannan aiki da suka yi.
Sannan ya tabbatar musu da cewa zai duba dukkanin shawarwarin su tare da ɗaukar matakin da ya dace cikin gaggawa.
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin Ganduje Ta Maida Martani Kan Shirin Hana Mata Tukin Mota a Ƙano
Gwamnatin jihar Kano, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa babu wani shiri na hana mata tukin mota a jihar, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan yaɗa labarai, Muhammad Garba, shine ya faɗi haka yayin da yake martani kan jita-jitar dake yawo cewa gwamnatin jihar na shirye-shiryen kafa dokar hana mata tuki.
Asali: Legit.ng