Gwamnonin APC sun kira taron gaggawa kan makomar shugabannin Jam'iyya da zaben gobe

Gwamnonin APC sun kira taron gaggawa kan makomar shugabannin Jam'iyya da zaben gobe

  • Ana sa rai cewa na jima gwamnonin jam’iyyar APC za su yi zama a garin Abuja
  • Gwamnonin za su tattauna a kan abin da ya shafi hallacin kwamitin rikon kwarya
  • Bayan zaman ne za a dauki mataki game da zabukan da jam’iyyar ta tsara a gobe

Abuja- Gwamonin jam’iyyar APC mai mulki za su yi wani taro na gaggawa a yau Juma’a, 30 ga watan Yuli, 2021, a babban birnin tarayya da ke Abuja.

Rahotanni daga jaridar Punch sun bayyana cewa gwamnonin za su zauna ne a game da shirin zaben shugabannin da aka shirya za ayi a jihohi a gobe.

Hakan ya zama dole bayan kotun koli ta yi hukuncin da ke nuna rashin halaccin nada gwamna Mai Mala Buni a matsayin shugaban jam’iyya na riko.

Yau APC za ta san makomarta - Dalori

Shugaban APC na Borno, Ali Bukar Dalori, ya shaida wa jaridar cewa APC za ta san makomar ta ne bayan wannan zama na musamman da za ayi an jima.

Kara karanta wannan

Mailafia: Hana saida wa ‘yan canji Dalar Amurka zai kara rugurguza darajar Naira a Najeriya

“Gwamnoni za su yi taro gobe (Juma’a), saboda haka ba zan iya cewa ko za a shirya wannan zabe, ko kuma za a dakata ba.”
“Gwamnonin sun tafi Abuja domin ayii zaman gaggawa a gobe. Bayan wannan zama, za a sa inda jam’iyyar APC ta sa gaba.”
“Ka da ku damu, zuwa gobe za a san abin da za ayi.”

Jam'iyyar APC
Manyan APC a wajen taro Hoto: Bashir Ahmaad
Asali: UGC

Amma wani babban lauya da ya kare APC a shari’ar Ondo, Adeniyi Akintola, ya ce babu inda kotu ta nuna rashin halaccin kwamitin su Mai Mala Buni.

Akintola SAN ya ce abin da mafi yawan Alkalan kotun koli suka zartar shi ne kwamitin ya na da gindin zama, ya ce ra’ayin sauran Alkalan bai da tasiri.

“Wannan ne hukuncin da kotun korafin zabe, kotun daukaka kara, da kotun koli suka yanke. Ban san dalilin kawo ra’ayin kalilan daga cikin Alkalan ba.”

Wasu kusoshin jam’iyya sun ce ka da ayi zabe a gobe

Kara karanta wannan

Bayan APC ta sha da kyar a kotu a zaben Gwamna, Minista ya ce za a iya rasa zaben 2023

An ji Hukuncin kotun kolin kasar ya neman rusa shirin Mai Mala Buni, inda wasu masu ba Shugaban kasa shawara suka ce a tarwatsa kwamtin CECPC.

Sanata Ita Enang, Sanata Babafemi Ojudu, Festus Keyamo da kuma Muiz Banire suna cikin masu bada shawarar a ruguza kwamitin rikon kwaryan da aka kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng