JAMB Ta Sake Shirya Jarabawar UTME 2021 Ga Wasu Dalibai, Ta Fadi Rana

JAMB Ta Sake Shirya Jarabawar UTME 2021 Ga Wasu Dalibai, Ta Fadi Rana

  • Hukumar JAMB ta sanar da sake shiryawa wasu ɗalibai jarabawa waɗanda suka samu matsala a jarabawar bana
  • Kakakin hukumar, Dr. Fabian Benjamin, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis
  • JAMB ta umarci ɗaliban da abun ya shafa da su sake fitar da takardarsu domin sanin lokaci da wuri

FCT Abuja - Hukumar JAMB ta sake shiryawa ɗalibai sama da 18,000 jarabawar share fagen shiga manyan makarantu UTME saboda wasu matsaloli da suka samu.

Punch ta ruwaito cewa JAMB ta ɗau wannan matakin ne ga ɗaliban da suka samu matsalar zanen yatsa da kuma waɗanda jarabawar ta haɗe musu da NABTEB.

This day ta rahoto cewa ɗaliban da abun ya shafa zasu rubuta jarawar ne ranar 6 ga watan Agusta a wasu zaɓaɓɓun wurare a faɗin ƙasar nan.

Kakakin hukumar JAMB, Dr. Fabian Benjamin, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Daliban Makarantar Sojoji da Dama

Dalibai na rubuta jarabawar JAMB
JAMB Ta Sake Shirya Jarabawar UTME 2021 Ga Wasu Dalibai, Ta Fadi Rana Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Banda waɗanda suka ga sakamakon su

Hukumar ta ƙara da cewa babu wani ɗalibi wanda ya zauna jarabawa kuma ya ga sakamakonshi da zata sake shirya wa jarabawa.

JAMB ta yi watsi da wasu rahotannin ƙarya da wasu kafafen watsa labarai ke yaɗawa game da sake shirya jarabawar.

Wani sashin jawabin yace:

"Zamu shirya bincike na musamman kan waɗanda zasu zauna jarabawar kuma duk wanda muka kama zamu gurfanar da shi."

Su waye zasu rubuta sabuwar jarabawar?

JAMB tace ɗaliban da aka sake shirya wa jarabawar sune waɗanda UTME 2021 ta haɗe musu da jarabawar kammala sakandire NABTEB, kuma aka mika kokensu ga JAMB.

Hakanan akwai waɗanda suka samu matsala wajen zanen yatsunsu a ranar rubuta jarabawar da kuma waɗanda tasu matsalar ta shafi NIN.

Yaushe za'a rubuta jarabawar?

Jawabin ya cigaba da cewa:

"Bayan gudanar da bincike da kuma nazari kan jarabawar UTME 2021 da aka kammala wacce aka samu nasarar yin ta.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Kasuwa Sun Garkame Shagunansu a Aba Saboda Shari'ar Nnamdi Kanu

"Hakanan bayan tattauna da hukumar NECO kan jadawalin jarabawarta da ake gudanarwa a yanzun, JAMB ta yanke cewa za'a gudanar da jarabawar ranar 6 ga watan Agusta."
"Muna umartar ɗaliban da abun ya shafa su sake fito da takardarsu domin ganin lokaci da kuma wurin da zasu rubuta jarabawar."

A wani labarin kuma Gwamna Buni Ya Yi Watsi da Hukuncin Kotun Koli, Ya Na Nan Daram a Shugaban APC

Sakataren kwamitin riko na jam'iyar APC ta ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya bayyana cewa gwamna Mai Mala Buni zai cigaba da jagorancin kwamitin riko na jam'iyyar.

Akpanudoedehe ya faɗi haka ne yayin taron manema labarai a sakateriyar APC ta ƙasa ranar Alhamis 29 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: