2023: ‘Yan Najeriya na Allah-Allah PDP ta dawo, In ji Atiku yayin da ya hadu da Wike don yin sulhu

2023: ‘Yan Najeriya na Allah-Allah PDP ta dawo, In ji Atiku yayin da ya hadu da Wike don yin sulhu

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya ziyarci gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike
  • Atiku ya kai ziyarar ne domin su yi sulhu tare da dinke banbancin da ke tsakaninsu gabannin zaben 2023
  • Ya kuma bayyana cewa 'yan Najeriya sun matsu 2023 ta zo don PDP ta karbi shugabancin kasar daga hannun jam'iyya mai mulki

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya gana da Gwamnan Ribas, Nyesom Wike a Fatakwal don sasanta rikicin da ke tsakaninsu gabanin babban zaben na 2023, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ziyarar da Atiku ya kai wa Wike ita ce ta farko tun bayan da ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sabanin dan takarar da Wike ke so wato gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal a 2015.

2023: ‘Yan Najeriya na Allah-Allah PDP ta dawo, In ji Atiku yayin da ya hadu da Wike don yin sulhu
Atiku ya ce 'yan Najeriya sun matsu su ga PDP ta dawo mulki a 2023 Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kwanan nan aka ruwaito cewa Wike da Atiku sun sha banban a gwagwarmayar da ake kan makomar Prince Uche Secondus a matsayin Shugaban PDP na kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni Ya Yi Watsi da Hukuncin Kotun Koli, Ya Na Nan Daram a Shugaban APC

Yayin da aka ce Wike yana kokarin ganin an tsige Secondus, Atiku ya nuna goyon bayan ci gaba da rike shi a matsayin Shugaban jam’iyyar.

Amma wata sanarwa daga mataimakin Wike na musamman a bangaren yada labarai, Kelvin Ebiri, ta ambato Atiku yana bayyana dalilan ziyarar tasa.

Atiku, wanda ya yi magana a gidan gwamnati, Fatakwal, ya ce ganawarsa da Wike ta cimma nasara, yana mai bayanin cewa al'amuran jam'iyyar ne suka kawo shi jihar.

Ya ce musamman ya dauki lokaci tare da Wike don sasanta batutuwa kan yadda za a tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali a PDP don ba jam’iyyar damar samun nasarar zabe a 2023.

Ya ce 'yan Najeriya suna jiran PDP ta karbi mulki a matakin tarayya a 2023.

Atiku ya ce:

“To, na zo nan ne don in yi sulhu da gwamnan kan lamuran jam’iyyar da kuma yadda za mu tabbatar da cewa akwai hadin kai da kwanciyar hankali a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Masoya Atiku a jihar Kano sun fara rabawa Kanawa burodi da sunan kamfe

"Don mu samu damar karbar mulki a 2023. Na yi imanin cewa 'yan Najeriya na Allah-Allah 2023 ta zo, don PDP ta dawo."

Atiku ya bayyana matsalar rashin tsaro a kasar a matsayin mummunan lamari, yana mai cewa PDP za ta bayyana manufofinta kan yadda za ta magance lamarin a lokacin da ya dace.

Ya ce:

“Ban taba ganin (rashin tsaro) mai munin wannan ba. Na shekara 70 da ‘yar doriya, ban taɓa ganin abubuwa sun munana haka ba ta fuskancin tsaro, tattalin arziki da rashin aikin yi. Wannan shi ne mafi munin.
“Me zai hana ku ba mu lokaci? Zamu fito da manufofinmu. Za mu gabatar da su ga ’yan Najeriya idan lokaci ya yi.
“Mun yi hakan a baya. A karkashin PDP, mun samu ci gaban tattalin arziki mafi girma, mun rage rashin aikin yi. Kun san cewa za mu iya yin hakan.”

Ya yaba da gagarumar nasarar jagoranci da Wike ya samu, wanda ya bayyana a matsayin Babban Gwamna a tsakanin takwarorinsa a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Ikedi Ohakim: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu a jihar Imo

Ya kuma yaba wa Gwamnan kan irin shugabanci da kuma aikin da yake yi a kan karagar mulki.

A wani labarin kuma, masoya ga tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, sun fara rarraba burodi, wanda ake wa lakabi da ‘Atiku Kawai’ ga mazauna Jihar Kano.

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da ake ikirarin cewa Atiku na neman tsayawa takarar shugaban kasa gabanin zaben 2023, duk da cewa bai fito fili ya tabbatar da hakan ba, SaharaReporters ta ruwaito.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya fara neman mukamin mafi girma tun shekarar 1993.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng