Wani hamshakin attajirin Najeriya ya ziyarci kamfaninsa, ya baiwa ma'aikata manyan kudade a cikin bidiyo

Wani hamshakin attajirin Najeriya ya ziyarci kamfaninsa, ya baiwa ma'aikata manyan kudade a cikin bidiyo

  • Shahararren attajirin nan na Najeriya, Marksman Chinedu Ijiomah ya gwangwaje ma'aikata a daya daga cikin kamfaninsa yayin da ya ziyarce su
  • Dan kasuwar ya zaburar da ma'aikata tare da rera wakoki masu karfafa gwiwa sannan ya ci gaba da raba kudade masu daraja ga kowane daya daga cikinsu
  • Ma'aikatan da suka cika da farin ciki sun nuna mamakin wannan karimcin nasa yayin da wasu suka durkusa a kasa yayin da kudin ya shiga hannusu

Shugaban kungiyar Chinmark Marksman Chinedu Ijiomah ya haifar da hayaniya a daya daga cikin kamfanoninsa lokacin da ya kai musu ziyarar gani da ido.

A wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafinsa na Facebook, attajirin ya fara ne da kakkausan kalamai masu karfafa gwiwa wadanda suka shafi manufar kamfanin.

Wani hamshakin attajirin Najeriya ya ziyarci kamfaninsa, ya baiwa ma'aikata manyan kudade a cikin bidiyo
Ya karfafa wa ma'aikata gwiwa ta hanyar raba masu kudi Hoto: Marksman Chinedu Ijiomah
Asali: Facebook

Yayinda ma'aikatan da ke cike da farin ciki suka amsa da karfin gwiwa, sai ya fito da kudi masu daraja daga aljihun rigarsa sannan ya mikawa kowanne ma'aikaci.

Kara karanta wannan

Dillalan shanu na neman filin kiwo mai girman murabba'in mita 30000 a wata jihar kudu

Ma'aikatan da suka dimauce sun faɗi kasa a lokacin da suka karɓi kudaden, inda suka nuna tsantsar farin ciki ga wannan karamci nasa.

Masu amfani da shafin soshiyal midiya sun jinjinawa wannan karamci nasa

Usman Okutepa ya ce:

"Mista Marksman, kai babban mutum ne ba wannan kadai ba kai mai karfafa gwiwa da zaburarwa ne. Allah ya kara maka lafiya yallabai."

Jerry Wealth Ochomma ya ce:

"Jinjinawa kokarin ma’aikata abu ne mai kyau ... #Kana kokari sosai Marksman ..."

Chidinma Ikoro ta rubuta:

"Kuɗi na kawo farin ciki duba da yadda suke murmushi lokacin da suka ga kuɗaɗen masu daraja. Allah ya albarkace ka yallaɓai."

Adaobi Samuelson ta ce:

"Ana bukatar karfafa gwiwa a kowane lokaci a kamfani kuma haka abun yake.
" Chinmark ga duniya."

A wani labari na daban, wani bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ga wasu manyan yara suna jefa kudi a sama a wajen wani bikin aure a Benin, babban birnin jihar Edo.

Kara karanta wannan

Dalilai da ke nuna alamun Nnamdi Kanu na iya fuskantar hukuncin kisa ko daurin rai da rai

Yaran sun fito da damin kudi masu yawa inda suka dunga jefa su a iska sannan kuma an gano baƙi da suka hallara suna ta dibar rabonsu.

A bidiyon da aka wallafa a shafin Instagram ta @instablog9ja, an ga yaran ma a filin suna ta yi wa wasu baƙi liki yayin da kudade suka cika filin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel