Da Duminsa: Duk da Umarnin Alkali, DSS Ta Gaza Gurfanar da Hadiman Sunday Igboho Dake Tsare

Da Duminsa: Duk da Umarnin Alkali, DSS Ta Gaza Gurfanar da Hadiman Sunday Igboho Dake Tsare

  • Hukumar DSS ta gaza gurfanar da hadiman Sunday Igboho, dake tsare hannunta duk da umarnin kotu
  • Babbar kotun tarayya dake Abuja ta umarci DSS ta gabatar da hadiman ranar Alhamis 29 ga watan Yuli
  • A halin yanzu Alkalin kotun ya ɗage zaman zuwa 2 ga watan Agusta tare da umarnin a kawo mutanen

FCT Abuja:- Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi watsi da umarnin kotu na kawo hadiman shugaban yan awaren kafa kasar yarbawa, Sunday Igboho, gaban kotu, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Mai shari'a Obiora Egwuatu na babbar kotun tarayya dake Abuja ya umarci DSS ta gurfanar da hadiman Igboho 12 dake tsare a hannunsu ranar 29 ga watan Yuli.

Rahoton Punch ya nuna cewa za'a cigaba da shari'ar mutanen duk da cewa kotun ta tafi hutun shekara-shekara wanda ta fara daga 26 ga watan Yuli.

Sunday Igboho
Da Duminsa: Duk da Umarni Alkali, DSS Ta Gaza Gurfanar da Hadiman Sunday Igboho Dake Tsare Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yaushe DSS zata kawo hadimai 12?

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Dage Sauraron Karar Sheikh Abduljabbar, Zai Cigaba da Zama a Gidan Gyaran Hali

Bayan gazawar hukumar DSS na kawo mutanen gaban kotu yau Alhamis, Mai shari'a Egwatu ya sake baiwa hukumar umarni tare da ɗage zaman.

Alkalin ya umarci DSS da ta gabatar da hadiman Sunday Igboho 12 dake hannunta ranar Litinin 2 ga watan Agusta.

Yayin da yake bada sabon umarnin, Alkalin yace:

"Idan babbar kotu ta bada wani umarni, to ya zama wajibi a girmama wannan umarnin kuma a mata biyayya."

Alkali Egwatu ya umarci DSS da ta samarwa majalisar lauyoyin mutum 12 lokacin da zasu gana daganan zuwa ranar Litinin.

Tun farko dai waɗanda ake zargin ne suka shigar da ƙarar hukumar DSS kan cewa an tauye musu haƙƙinsu na yan adam.

A wani labarin kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Cafke Wani Tsageran IPOB Dauke da Muggan Makamai

Rundunar yan sanda ta jihar Imo, tace ta cafke wani da ake zargin mamban kungiyar ESN-IPOB ne ɗauke da makamai.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yi Watsi da Wata Bukatar Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

Kakakin hukumar yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, shine ya bayyana haka, yace an kwato sinkin alburusai a hannunshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel