Allah Ya Isa Ban Yafe Ba, Fitacciyar Jarumar Kannywood Ta Yi Martani Ga Masu Sukarta

Allah Ya Isa Ban Yafe Ba, Fitacciyar Jarumar Kannywood Ta Yi Martani Ga Masu Sukarta

  • Jaruma Mansura Isa, ta yi raddi cikin fushi ga masu zaginta da sukarta bayan rabuwarta da mijinta
  • Mansura ta nuna rashin jin daɗin kan yadda wasu suke sukarta tare da kiranta da sunaye daban-daban
  • A watan Mayun da ya gabata ne auren jarumar wanda ya ɗau tsawon shekara 13 ya zo karshe

Mansurah Isah, Tsohuwar matar fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood, Sani Danja, ta yi kira ga masu sukarta da su dakata hakanan da kiranta da wasu sunaye sabida ta zama bazawara, kamar yadda premium times ta ruwaito.

Mansura, wanda ta fara shirin fina-finai a ƙarshen shekarar 1990, da tsohon mijinta sun gina auren soyayya kafin su rabu a watan Mayun da ya gabata, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A ranar Laraba, jarumar ta yi martani ga masu sukarta a wani rubuta da a buga a shafinta na kafar sada zumunta Instagram.

Jaruma Mansura Isa ta yi martani ga masu Sukarta
Bayan Rabuwa da Mijinta, Fitacciyar Jarumar Kannywood Ta Yi Martani Ga Masu Sukarta Hoto: @Mansurah_Isah
Asali: Instagram

A rubutun da ta yi, fitacciyar jarumar ta buƙaci masu sukarta da su fita daga cikin al'amuran rayuwarta.

Kara karanta wannan

‘Yan sanda sun yi ram da wasu maza biyar da ke lalata da junansu a Kano

Tace: "Hmm, nayi hoton sallah, kunce abinda yasa na fito kenan, nayi tafiya zuwa wani gari kunce abinda yasa na kashe aurena kenan, naje cin abinci da ƙawayena kunce iskancin da nake son yi kenan."

"Naje aikin NGO na rabo wanda na saba yi yau shekara wajen 20 kenan inayi, kunce daman yawon da ya fito da ni kenan."

"Inason ku sani cewa ban damu ba, zan yi duk abinda naga dama rayuwata ce. Wai miye sabo? kalmar saki ce baku taba ji ba ko kuwa baku taɓa ganin macen da aka saka ba?"

Ba nice ta farko ba

Hakanan kuma, Mansura ta yi kira ga masu sukarta da su barta ta sakata ta wala domin ba itace mace ta farko a masana'antar Kannywood da aka saka ba.

Tace: "Manzon Allah (SAW) ya taɓa sakin matarsa, Allah SWT ya halarta saki a musulunci, to miye sabo? wasu harda bude sabon shafi don su zage ni, hakanan kawai, to ni ban damu ba."

Kara karanta wannan

Hotunan wasu 'yan Najeriya 4 wadanda suka dawo da miliyan N152.4 da aka tura asusun bankunansu bisa kuskure

"Yara da tsofaffi suna bina ta shafina suna zagina, ku je ku tambayi iyayenku mata, yan uwanku da maƙotanku waɗanda aka saka yaya ake ji, ba zan taba yafewa duk wanda ya zage ni ba, Allah ya saka mun."

Asalin auren su

Tsofaffin ma'auratan sun haɗu ne a masana'antar shirya fina-finai a farkon shekarar 2000, kuma sun yi aure shekara 13 da suka gabata, Allah ya aazurtasu da samun ƴaƴa huɗu.

Sai dai lamarin auren nasu yayi muni a watan Mayu, inda Mansura ta bayyana rabuwarsu a kafar sada zumunta ta instagram a cikin watan.

Labarin rabuwar masoyan ya zama babban abin tattaunawa ga masu bibiyar jaruman Kannywood ɗin da sauran abokan sana'a.

Mafi yawancin masu suka suna zargin jaruma Mansura da cewa: "Ita ta tilasta rabuwarsu da mijinta."

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262