Jiga-jigan PDP masu rashawa ne ke komawa APC, In ji Gwamna Tambuwal
- Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya bayyana cewa jiga-jigan jam’iyyar PDP masu cin hanci da rashawa ne kawai suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki
- Tambuwal ya sha alwashin cewa za su kwato mulki daga hannun jam'iyya mai mulki a 2023
- Ya kuma bayyana cewa za su ceto kasar tare da inganta ta zuwa ga tafarkin ci gaba
Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya ce jiga-jigan jam’iyyar masu cin hanci da rashawa ne kawai suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Tambuwal ya kuma ce wadanda suka sauya shekar sun koma APC ne don gujewa gurfanar da su kan rashawa, jaridar The Nation ta ruwaito.
Gwamnonin PDP, wadanda suka yi tattaki zuwa Bauchi don tattaunawa kan halin da kasa ke ciki, sun yi Allah wadai da abin da suka bayyana da "amfani da dabarun makarkashiya don karkatar da gwamnonin PDP su shiga APC."
Sun sake nanata kudurin su na samar da sakamakon zabe ta hanyar na’ura, inda suka bukaci Majalisar Dokoki ta kasa da ta yiwa dokar zabe kwaskwarima.
Taron wanda gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya karbi bakuncinsa ya samu jagorancin Tambuwal. Sun kuma tattauna kan matsalolin tattalin arziki da tsaro da kasar ke fuskanta da rikicin da ke damun jam'iyyar adawa.
Tambuwal, wanda ya samu wakilcin takwaransa na jihar Taraba, Darius Ishaku, ya yi magana a liyafar dare da aka gudanar a dakin taro na Gidan Gwamnatin Bauchi, ya ce PDP za ta sake dawowa kan mulki a 2023.
Ya ce:
“Ba mu da wani fata, sai a PDP. Za mu zauna a cikin PDP, za mu ceto duk abin da yayi saura a kasar idan muka sake dawowa kan mulki a 2023.
"Idan ka duba, a cikin jihohin PDP ne kawai ayyukan ke gudana. Ina magana ne da hujjoji da kuma zukatan ‘yan Najeriya da yawa.
“Wadanda ke guduwa suna barin PDP ne zuwa inda aka gafarta musu zunubansu… Don haka, idan kai mugu ne kuma mai rashawa, ka wuce zuwa APC inda za a gafarta maka zunubanka, amma ba mu yarda ba kuma ba mu aminta da tsoratarwa ba. Za mu ci gaba da kasancewa a cikin PDP, za mu kwace mulki kuma mu inganta Najeriya.”
A karshe gwamnonin PDP sun yi martani, sun bayyana matsayinsu kan tura sakamakon zabe ta na’ura
A gefe guda, yayin da ake takaddama kan kin amincewa da watsa sakamakon zabe ta na'ura da majalisar dattawa ta yi, kungiyar gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta mayar da martani a karshe.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnonin, sun nace cewa dole ne Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da yada sakamakon zaben ta na'ura.
A martaninsu, gwamnonin PDP sun dage kan lallai sai Majalisar Kasa ta samar da dokoki don ganin yiwuwar hakan.
Asali: Legit.ng