Shehin Malamin Musulunci, Gumi ya bukaci Shugaban kasa Buhari ya gaggauta murabus

Shehin Malamin Musulunci, Gumi ya bukaci Shugaban kasa Buhari ya gaggauta murabus

  • Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi tir da Gwamnatin Muhammadu Buhari
  • Malamin ya ce gwamnatin tarayya ta gagara kare rayuka da dukiyoyin al’umma
  • Shehin ya yi irin kiran da ya yi a baya, ya bukaci shugaban kasa ya yi murabus

Kaduna - Malamin addinin musulunci, Ahmad Abubakar Gumi, ya nemi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi murabus saboda matsalar tsaro.

Gwamnatin Najeriya ba ta kare al'umma ba - Ahmad Gumi

Sahara Reporters ta rahoto Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya na cewa gwamnatin da shugaba Muhammadu Buhari yake jagoranta ta gaza kare Bayin Allah.

Shehin malamin ya ce jinanan al’umma ya na ta kwarara a jihohin kasar nan saboda rashin tsaro.

Ahmad Abubakar Gumi ya ce irin wannan shawarar ya bada a lokacin da Goodluck Jonathan yake mulki, don haka ya maimaita ta ga Muhammadu Buhari.

Bidiyon da babban malamin ya yi wannan bayani ya shiga hannun jaridar ne a ranar Talata, 27 ga watan Yuli, 2021, amma Legit.ng ta lura an dade da yin wa'azin.

Kara karanta wannan

Abduljabbar: Sheikh Maqary ya yi karin haske bayan wasu kalamansa sun tada kura

Gara abin da ya faru a lokacin da Goodluck Jonathan yake mulki

“A mulkin Jonathan lokacin da jini ya ke kwarara, na soke shi saboda bai yi abin da ya kamata ba. Abin da ya sa na zargi Jonathan da laifi shi ne Boko Haram suna ta dasa bam a ko ina, gwamnati ta ki yin abin da ya dace.”

Dr. Gumi
Ahmad Abubakar Mahmud Gumi Hoto: www.rfi.fr/ha
Asali: UGC

“Saboda an yi kashe-kashe a gwamnatinka, don haka laifin kisan ya na hannunka, idan ka yi bakin kokarinka, sai in ce Allah zai iya yafe maka, amma ba ka damu ba, Allah ba zai yi maka gafara ba.”

Ahmad Gumi ya ce abin da ya ke faru wa yau ya zarce kashe-kashen da aka yi a baya, amma shugabanni ba su damu ba, suna yawan zuwa biki a garuruwa.

“Sai ka yi wa kanka adalci da kanka. Addininmu ya na koyar da adalci. A lokacin Jonathan ana zubar da jini a masallatai da cooci da unguwanni, na ce ya yi murabus saboda ya gaza, na ce ya sauka daga mulki da gaggawa.”

Kara karanta wannan

Mutumin da ya yi yunkurin kashe shugaban kasar Mali ranar sallah ya mutu a magarkama

Dr. Gumi ya ce ya na da zabi biyu ne rak, ko dai ya nemi afuwar Jonathan na sukarsa da ya yi, ko ya bukaci Buhari ya sauka daga mulki kamar yadda ya yi a baya.

Kwanakin baya ne aka ji cewa ganin yadda ake fama da matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya, babban malamin ya shiga har zuwa inda ‘yan bindiga suke.

Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya lallabi wadannan miyagu su daina kashe jama'a, sannan ya roki gwamnatin tarayya ta yi masu afuwar duk barnar da suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel