Abduljabbar: Sheikh Maqary ya yi karin haske bayan wasu kalamansa sun tada kura

Abduljabbar: Sheikh Maqary ya yi karin haske bayan wasu kalamansa sun tada kura

  • Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari ya yi magana game da Abduljabbar Nasiru Kabara
  • Kalaman babban limamin sun jawo hayaniya, har Dr. Gadon-Kaya ya yi masa raddi
  • Shehin ya maida martani a shafinsa na Facebook, inda ya fayyace abin da yake nufi

Kwanan nan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari ya yi wasu kalamai da ake ganin sun bar baya da kura a Najeriya.

Abduljabbar na neman kare Annabi SAW ne amma ... - Maqary

Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari ya tofa albarkacin bakinsa a game da muhawarar da wasu malamai su ka yi da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a Kano.

Limamin babban masallacin Juma'an na babban birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa a ta sa fahimtar, babu hukuncin ridda a kan Abduljabbar Nasiru Kabara.

Shehin malamin ya yarda cewa Abduljabbar Kabara ya ci mutuncin Sahhaban Manzon Allah, sannan ya bata ma’aika, amma ya yi masa uzuri da jahilci.

Kara karanta wannan

A gaskiya Gwamna Ganduje ya na mana shisshigi a shari’ar Abduljabbar Kabara inji Lauyoyinsa

Babban malamin ya ce Abduljabbar Kabara ya na kokarin kare Manzon Allah (SAW) ne a kan bata.

Sai dai Dr. Abdallah Umar Gadon-Kaya ya na ganin Ibrahim Ahmad Maqari ya na kokarin wanke Abduljabbar Kabara ne a lokacin da duk aka yi masa rubdugu.

Sheikh Maqary da Gadon Kaya
Sheikh Ibrahim Ahmad da Dr Abdallah Gadon-Kaya
Asali: UGC

Gadon-Kaya: Ya kamata a taka wa Farfesa Maqary burki haka nan

Abdallah Umar Gadon-Kaya ya zargi malamin da yawan kawo ra’ayin da suka saba wa sauran malamai a duk lokacin da wani abu irin haka ta faru a kasa.

A hudubarsa ta Juma’a, 23 ga watan Yuli, 2021, Gadon-Kaya ya ce suna da faifan malamin inda ya yi wasu kalamai kan wanda ya yi wa Annabi batanci a Kano.

A wannan huduba, Abdallah Gadon-Kaya ya ce limamin bai kamata ya rika fito da akidarsa ba domin ya na limanci ne a babban masallaci na kasa baki daya.

Da yake maida martani a Facebook, duk da ya ce bai so hakan ba, Maqary ya kare kansa, ya yi karin haske kan cewa da ya yi bai wani saurari Abduljabbar ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan mako daya a Daura

Ibrahim Maqari ya ce hukuncin zagin Ma’aiki (SAW) ba zai yi aiki a kan malamin ba, ya kuma fayyace abin da yake nufi da cewa akwai ‘boyayyar manufa’.

A jiya ne aka samu labari cewa lauyoyin shehin malamin nan, Abduljabbar Nasir Kabara sun ce gwamnati na yi wa shari’ar da ke gaban kotu katsalandan.

Barista Saleh M. Bakaro ya ce bai kamata Gwamnan Kano ya fito, ya na magana kafin a kammala shari'a ba. Bakaro ya bukaci jama'a su sa wa gwamnati idanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel