Ba Bu Wanda Zai Tsoratar Da Mu Domin Mu Shiga APC, Gwamnonin PDP

Ba Bu Wanda Zai Tsoratar Da Mu Domin Mu Shiga APC, Gwamnonin PDP

  • Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto ya ce sauran gwamnonin PDP ba za su yarda a tsoratar da su su shiga APC ba
  • Shugaban kungiyar gwamnonin na PDP ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wurin taron da gwamnonin suka yi a jihar Bauchi don shiryawa zaben 2023
  • Tambuwal ya kuma yi ikirarin cewa sauran gwamnonin PDP da suka koma APC sunyi hakan ne saboda tsoron kada a bincike rashawar da suka tafka

Shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Waziri Tambuwal, ya yi zargin cewa gwamnonin da suka koma jam'iyyar All Progressive Congress (APC) sunyi hakan ne don kada a bincike rashawar da suka tafka.

A cewar rahoton na The Nation, Tambuwal ya bayyana cewa sauran gwamnonin PDP ba za su tsorata ba.

Ba Bu Wanda Zai Tsoratar Da Mu Domin Mu Shiga APC, Gwamnonin PDP
Gwamnonin Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP: Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Tambuwal, wanda ya samu wakilcin gwamnan Taraba, Darius Ishaku, ya yi magana ne a ranar Lahadi wurin taron da aka gudanar da gidan gwamnatin jihar Bauchi yayin yi wa gwamnonin Maraba zuwa jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP: Buhari ya mayar da fadar shugaban kasa sakateriyar APC

The Nation ta ruwaito cewa gwamnonin sun tafi jihar Bauchi ne don yin taro kan shirin tunkarar zaben 2023 da ke tafe inda gwamna Bala Mohammed ya basu masauki a jiharsa.

Gwamnonin da suka hallarci taron sun hada da Okezie Ikpeazu (Abia); Ahmadu Fintiri (Adamawa); Udom Emmanuel, (Akwa Ibom); Douye Diri (Bayelsa); Samuel Ortom (Benue).

Sauran sun hada da Ifeanyi Okowa (Delta); Godwin Obaseki (Edo); Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu); Seyi Makinde( Oyo); Nyesom Wike( Rivers) da mataimmakin gwamnan jihar Zamfara Mahdi Aliyu.

Tambuwal ya ce PDP ce kawai za ta iyo ceto Nigeria daga halin da ta shiga kuma za ta karbi mulkin kasa a 2023 don inganta rayuwar yan kasar.

Tambuwal ya soki APC kan rashin magance matsalar tsaro

Ya kuma soki gwamnatin tarayya kan gaza cin galaba kan Boko Haram cikin watanni shida kamar yadda ta yi alkawari, sai dai abubuwa kara tabarbarewa suka yi.

Kara karanta wannan

An gagara dinke barakar da ta shiga PDP duk da Gwamna ya zauna da Wike, Secondus

Gwamnan Sokoton ya ce:

"Wadanda suka ce za su gama da Boko Haram cikin watanni 6, gashi yanzu shekaru 6 kuma abin sai kara tabarbarewa ya ke yi.
"Yanzu muna da Boko Haram daban-daban suna adabar mu a kasar. Za mu zo mu mayar da Nigeria abin da ya dace ta zama. Abin alfahari a Afirka."

Asali: Legit.ng

Online view pixel