Yanzu-Yanzu: An yi ram da Sowore yayin da ake ci gaba da shari'ar Nnamdi Kanu

Yanzu-Yanzu: An yi ram da Sowore yayin da ake ci gaba da shari'ar Nnamdi Kanu

  • An kame Sowore a bakin babbar kotun tarayya dake Abuja yayin da ake jiran shari'ar Nnamdi Kanu
  • Jami'an tsaro sun cafke Sowore ne tare da wasu masu nuna goyon baya ga shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
  • Hakazalika. an fatattaki wasu magoya bayan Nnamdi Kanu yayin da suka hallara a bakin kotun

An kama Omoyele Sowore, mai gidan jaridar Sahara Reporters a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yayin da kotu ta ke ci gaba da shari’ar shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

An tattaro cewa jami’an tsaro sun cafke dan gwagwarmayar ‘Buhari-Must-Go’ a harabar kotun yayin da yake daukar bidiyon kai tsaye na Facebook da safiyar Litinin, Punch ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: An yi ram da Sowore yayin da ake ci gaba da shari'ar Nnamdi Kanu
Omoyele Sowore | Hoto: Omoyele Sowore
Asali: Facebook

A baya an bayar da rahoton cewa an sanya tsauraran matakan tsaro a kusa da kotun yayin da ake ci gaba da shari’ar Kanu, wanda ya kasance a hannun jami’an DSS a yau.

Kanu, wanda tun farko aka dawo da shi Najeriya daga wata kasar waje, yana fuskantar tuhume-tuhume masu alaka da ta'addanci a gaban Mai shari'a Binta Nyako.

Kara karanta wannan

Labari Da Ɗuminsa: Kotu Ta Tura Sunday Igboho Gidan Yari a Kwatano

'Yan jarida a kofar kotun, jami'an DSS sun hana su shiga kotun a kan cewa ba a ba su izinin ba su rahoton shari'ar ba.

An kuma ruwaito cewa 'yan sanda na sirri sun hana wasu kungiyoyin 'yan jarida daukar rahoto kan shari'ar shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu, yayin da ake ci gaba da shari'arsa a yau.

'Yan sanda sun cafke wasu 'yan kungiyar IPOB

‘Yan sanda a ranar Litinin sun fatattaki wasu mambobin kungiyar IPOB wadanda suka mamaye Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja don jin yadda za ta kaya a shari’ar Nnamdi Kanu, shugabansu.

Mambobin kungiyar da suka fusata sun mamaye kotun gabanin shari’ar tasa, inda wani rahoton The Cable ya ce tuni an kame wasu daga cikin mambobin na IPOB.

'Yan kungiyar IPOB din suna ta rera taken nuna goyon baya ga Kanu tare da neman a sake shi.

Shari'ar Kanu: An saki Sowore da magoya bayan Nnamdi Kanu bayan sun ci duka

Kara karanta wannan

Shari'ar Kanu: An saki Sowore da magoya bayan Nnamdi Kanu bayan sun ci duka

A wani labarin, Rahoto ya bayyana cewa, an saki mawallafin jaridar SaharaReporters Omoyele Sowore da wasu da aka kama yayin wata zanga-zanga a Babbar Kotun Tarayya, jaridar Punch ta ruwaito.

Masu fafutukar sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ke fuskantar shari'a a kotu. ‘

Yan sa’o’i kadan bayan kamasu, dan fafutukar 'Buhari-Must-Go' ya sanar da cewa an sake shi tare da wasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel